Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya yi kakkausar ga kawancen dakarun kasashen duniya a karkashin jagorancin Amurka, dangane da yadda ya kasa murkushe mayakan da ke da’awar jihadi a kasashen Syria da Iraki.
Sarkozy wanda ke gabatar da jawabi gaban magoya bayan jam’iyyarsa a birnin Paris, ya ce rundunar kawance ta rasa jagoranci nagari ne, kuma hakan ne babban dalilin da ya sa mayakan IS suka samu nasarar kutsawa tare da lalata garin Palmyra mai cike da tarihi.
Har ila yau Sarkozy wanda ya shugabanci Faransa daga 2007-2012, ya kare Faransa a lokacin mulkinsa da kuma Birtaniya dangane da rawar da suka taka, wajen kawar da Mu’ammar Kaddafi daga shugabancin Libya, inda ya ce ko ba komai bayan kifar shugaban, an shirya ingantaccen zabe a watan yulin 2012 wanda aka samu fitowar jama’a akalla kashi 60%.
Title :
Sarkozy ya soki kawance da ke fada da mayakan IS
Description : Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya yi kakkausar ga kawancen dakarun kasashen duniya a karkashin jagorancin Amurka, dangane da yadda ...
Rating :
5