Assalamu 'alaikum 'yan uwa Musulmi. Tun Kamar Watanni uku da suka gabata wasu 'yan uwa sake ta aikowa da tambayoyinsu a game da Sallar nan mai falala wacce ake kira SALATUT TASBEEHI.
Wadansu suna yin tambaya ne game da ita kanta sallar. wato yadda ake yinta. wadansu Mutanen Kumar suna tambaya ne akan INGANCIN HADISIN DA YAZO DA BAYANINTA.
To yanzu Insha Allahu zanyi bayani akan yadda ake yinta, sannan Kuma inyi magana akan hadisan da suka zo da banyaninta.
"Watarana Manzon Allah (saww) yace ma Baffansa Sayyiduna 'Abbas bn Abdil-Muttalib (rta):
'Ya Baffa!! Bari inyi maka zumunci! Bari inyi maka kyauta!! Bari in amfaneka"
Sai Abbas (ra) yace "Kwarai kuwa Ya Ma'aikin Allah".
Sai Manzon Allah (saww) yaci gaba da ce masa:
"Baffa kayi sallah raka'a 4. acikin kowacce raka'a ka karanta Fatiha da surah.
Bayan ka karanta surah sai kayi TASBEEHI guda goma sha-biyar (15) kafin kayi ruku'u.
Idan kayi ruku'u zaka maimaita (Tasbeehin) sau goma (10). Idan ka dago kanka (daga ruku'un) ma haka zakayi tasbeehin guda goma (10).
Sannan ka tafi Sujjadah. acikin Sujjadah zakayi tasbeehin guda goma (10). Idan ka dago daga Sujjadar ma haka zakayi tasbeehin sau goma.
Sannan ka sake yin Sujjadar. ita ma acikinta kayi tasbeehin sau 10. idan ka dago kanka daga wannan sujjadar (sujada ta 2) zaka sake yin tasbeehin guda 10 kafin ka mike tsaye.
Tasbeehi 75 kenan acikin kowacce raka'a, kuma 300 kenan acikin raka'a 4 gaba daya.
Ko zunubanka sun kai yawan adadin yashin da yake Aalij, to Allah za gafarta maka su."
Sai Sayyiduna Abbas (ra) yace "YA RASULALLAHI! waye zai iya aiwatar da irin wannan sallar akullum!"
Sai Manzon Allah (saww) yace "TO IDAN BA ZA IYA YI KULLUM BA, SAI KA RIKA YINTA DUK JUMA'A (wato duk mako guda kenan).
Idan ba zaka iya yi duk mako ba, to ka rikayi sau 'daya duk wata guda".
Bai gushe ba yana magana har sai da yace : "KAYI TA KODA SAU 1 NE ACIKIN SHEKARA GUDA".
YADDA AKE YIN TASBEEHIN: Allahu Akbar Wal-Hamdu lillah wa Subhanallah, ko kuma Subhanallah Wal hamdu lillah wa La'ilaha illal Lahu Wallahu Akbar (awata ruwayar).
★ Imam Tirmizy ne ya ruwaito wannan hadisin, acikin Jami'ut Tirmizy juzu'i na 2 shafi na 509.
Awajen Imamut Tirmizy yake cewa "An ruwaito hadisai da dama game da SALATUT TASBEEHI amma yawancin hadisan basu inganta ba. (Akwai rauni awajen masu ruwayar).
★ IMAM ABU-DAWUD shima ya ruwaito hadisin ta wata hanyar daban (wacce ba irinta Tirmizy ba. kuma Malamai sun HASSANA hadisin.
Aduba cikin SUNANU nasa, juzu'i na 2 shafi na 96, hadisi na 1,297.
★ IMAMUL HAKIM ya ruwaito irin wannan hadisin ta hanyar ABDULLAHI BN UMAR BN ALKHATTAB (ra). Kuma yace WANNAN HADISIN YA INGANTA. BABU WATA QURA-QURA ACIKIN ISNADINSA.
Daga cikin Hujjojin da suke tabbatar da INGANCIN HADISIN, shine yawaitar Sahabbai da Tabi'ai wadanda suke yin wannan Sallar, kuma suke koyar da ita ga Almajiransu.
ABDULLAHI IBNUL MUBARAK (RA) ya kasance yana yin wannan sallar kuma yana koyar da ita ga Almajiransa.
Kuma dukkan wadanda suka Ruwaito wannan Sallar daga Ibnul Mubarak, Mutane ne Ingantattu. kuma kowa yasan cewar Ibnul Mubarak ba zai koyar da duk abinda bai Inganta ba.
(Aduba cikin MUSTADRAKUL HAKIM ALA SAHIHAYNI juzu'i na daya, shafi na 464).
★ IMAM IBNU MAAJAH (rah) shima ya ware BABI GUDA ACIKIN LITTAFIN HADISINSA. wanda acikinsa yayi magana akan Salatut Tasbeehi tare da kawowa hadisai ingantattun daban daban.
(Aduba cikin Sunanu Ibni Maajah juzu'i na 1 shafi na 442, hadisi mai lamba 1,430)
★ IMAM ALBAIHAQEE (rah) shima bayan ya kakkawo hadisan da sukayi magana akan SALATUT TASBEEHI yace : "Kasancewar Salihan bayin Allah irinsu Ibnul Mubarak suna yinta, kuma an ruwaito ta daga garesu, Shima hujjah ne akan cewa hadisin Marfu'i ne kuma ya inganta.
(aduba cikin SHU'ABUL IMAN juzu'i na 1 shafi na 427).
★ IBNUL MUNDHIRY (RAH) shima ya ruwaito wannan hadisin sannan yace An ruwaito shi ta hanyoyi Sahihai masu yawa daga Sahabbai daban daban. Kuma Malaman Hadisi da dama sun inganta hanyoyin.
(aduba cikin ATTARGHEEB WAT TARHEEB juzu'i na 1 shafi na 267).
Albaniy yay Albaniy yay i kokarin raunata wata daga cikin Isnadan hadisin, yace wai akwai wani Majhuli acikin isnadin. Amma Malamai da dama suna sun mayar masa da maganarsa.
★ IMAM SUYUTY ya kawo sunayen Manyan HUFFAZU (maluma MAHADDATAN hadisi) sama da guda 20 wadanda suka inganta Hadisan SALATUT TASBEEHI. acikinsu akwai:
1. HAFIZ ABU SA'EED AS-SAM'ANY.
2. HAFIZ KHATEEB ALBAGHDADY.
3. HAFIZ IBNU MUNDAH.
4. HAFIZ IBNUS SALAH.
5. HAFIZ ABU MUSAL MADANY.
6. HAFIZ ZARKHASHY.
(Aduba cikin LA'ALI'UL MASNU'AH juzu'i na 2 shafi na 42 zuwa na 45).
A takaice dai SALATUT TASBEEHI ibadah ce mai falala wacce ruwayarta ta inganta daga Manzon Allah (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP