A kasidar da ya gabatar gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al- Makura kuma daya daga cikin 'yan kungiyar iyayen masu nakasa ta Najeriya yace sabuwar gwamnatin kasar zata inganta rayuwar nakasassu.
Yace kasar ta kuduri aniyar cigaban nakasassun kasar sabanin abun dake faruwa dasu can baya.
Gwamnan Tanko Al-Makura yace zasu yi uwa su yi makarbiya wajen ganin shugaban kasa Muhammad Buhari ya rabtaba hannu a dokar dake bada kariya ga masu nakasa ba tare da bata wani lokaci ba.
Yace yin hakan ya zama wajibi musamman idan aka yi la'akari da banbancin da ake nunawa nakasassu a Najeriya.
Yace a wannan tsarin da kasar ke tafiya ciki da kuma canjin al'amari da kasar ta samu kamata yayi al'ummar kasar su sake salo da sabon shiri wurin ganin yadda za'a tafi da kowa da kowa a cikin akushi daya musamman mutanen dake da nakasa.
Duk wanda yake da nakasa shi ma dan Adam ne kuma dan Najeriya ne. Yana da 'yanci daidai da kowa.
A nashi bangaren Dr..Lesley Robbins likitan kananan yara a sashen koyas da aikin likita na jami'ar Morehouse ta kasar Amurka cewa ya yi akwai bukatar Najeriya ta yi koyi da Amurka wajen tabbatar da bayar da ilimi kyauta ga masu nakasa da basu kariyar da ta dace tsakanin al'umma. Ta hakan za'a iya inganta rayuwar nakasassu a kasar.
Title :
Sabuwar Gwamnatin Najeriya Zata Inganta Rayuwar Nakasassu-inji Al-Makura
Description : A kasidar da ya gabatar gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al- Makura kuma daya daga cikin 'yan kungiyar iyayen masu nakasa ta Najeriya yace s...
Rating :
5