TAMBAYA TA 1639
********************
Salami alaikum warahamatullah, dafatan Mallam yasha ruwa lpy tareda iyalinshi? Allah yasa haka ameen. Mallam cikin satinda yawucema narubuto da irin wannan tambayar amma Allah baibada ikon amsawaba, Allah ne kawai zaibiyaka da irin namijin kokarinda kakeyi wajen ilmantar damu dabamu taimako babu abinda zamuce maka Mallam saidai Allah yabiyaka yasadaka da fiyyayen hallitta annabi muhammadu saw.
Mallam inada Marsala sosai, kwanakin baya nasha ganin masu irin matsalata suna turo fatawa anagayamasu abubuwanda zasunema surika amfani dashi kuma nima Mallam nakanbi sahunsu innema inrika amfani dashi amma Mallam wallahi matsalata haryanzu takici takicinyewa tanason kawomin barazana tazamantakewata da iyalina. Matsalar itace duk sadda zansadu da iyalina Mallam bana wuce seconds banakaiwa ko minti daya zanyi riliz. Mallam wallahi har kunyar matata nakeji ancemin basurne nayi maganin basur kuma ni kaina nasan banida basur, ancemin inyi test na ciwon zaki (sugar) duo bani dasu amma Mallam abin saigaba yake. Inayawan motsajiki Mallam, muna matukar wasa da juna nalokaci maitsawo Mallam amma wuyarta azzakarina yashiga shikenan sai riliz kuma zaikwanta bazai kara tashiba sai dogon lokaci kokuma nayi bacci nafarka. Mallam matata tafara gajiya dan Allah kataimaka min da magunguna da shawarwari. Nagode dalibinka ibrahim.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Akwai dalilai da dama wadanda sukan kawo ma Namiji raunin al'aurarsa. Misali kamar haka:
1. Shafar Aljanun soyayya. ajikinka ko jikinta.
2. Sihiri ajikinka ko jikinta.
3. chutar Sugar ko Hawan jini.
4. Raunin jijiyoyin al'aurar.
5. Basur ko Majina.
6. Istimna'i (wasa da hannu ajikin Al'aura).
Idan akwai daya daga cikin wadannan abubuwa, to dole ne anemi maganinsa idan har ana so asanu sauki da gaggawa.
Ga wasu Fa'idodi nan a jarraba:
1. Ka nemi garin KAMOUN, ka gaurayashi da man shanu ka rika shafawa a mazakutarka, Minti talatin kafin saduwa da iyalinka. Amma zaka je ka wanke da ruwan dumi kafin Jima'i. In sha Allahu zaka samu Qarfi da kuzari sosai.
2. Ka nemi garin Kustul Hindi cokali hudu, Garin Kuzbara cokali 3, Garin Habbatus sauda cokali biyu. Garin Citta da kanumfari cokali 1 da Rabi. Ka hadasu acikin ruwan zuma ka gauraya ka ajiye. Kullum da dare zaka rika shan cokali uku, Minti 20 jafin saduwa da iyali.
3. Ka yawaita shan kankana sosai kullum da magriba. Domin kankana tana Qara kuzarin Namiji. tana kunshe da sinadarai irin wadanda suke cikin Viagra.
Allah yasa a dache.
WALLAHU A'ALAM.