Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce rashin aikin yi ga matasa a kasar babbar matsala ce idan aka yi la’akkari da cewa fiye da rabin al’umar kasar matasa ne.
Buhari ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Aliyu Mustapha na Sashen Hausa na VOA inda ya ce wannan matsala ta shafi wadanda suka yi karatu da wadanda ma ba su yi ba.
“Wannan babbar matsala ce akan tafiyar zama lafiya a Najeriya saboda abubuwan da za su taimaka aga saukin neman aiki su ne sha’anin noma da sha’anin tono ma’adinai, wato kamar su zinare da azurfa wadanda Allah ya baiwa Najeriya su.” Inji Buhari
Buhari ya kara da cewa manyan kasashen duniya da ya gana da su a kasar Jamus, sun nuna sha’awarsu ta su taimaka a wadannan fannoni.
Daka aka tambayi shugaba Buhari shin ko hakan na nufin gwamnatinsa za ta nada matasa da mata a mukamai dabdan-daban, sai ya ce “ai batun yi musu aiki, ko suna cikin gwamnatin ko ba sa ciki dole a yi da su, kuma ma’aikata ai akwai matasa da mata a ciki.”
Ya kara da cewa “amma idan kana nufin mukamai na ministoci, ba zan ce da ‘yan uwa na tsoffi kadai za mu zamo a cikin gwamnati ba, dole a yi da masu jini a jiki." Ya ce.
Kwanaki 100 Na Farko
Shugaba Buhari ya ce abin da ya ke so gwamnatinsa ta fi maida hankali a kai cikin kwanakin 100 na farko shi ne ta samar da tsaro.
“To abin da na ke so mu yi, dama ni duk wurin yawon neman kuri’ata na fadi, sha’anin tsaro shi ne na daya, idan babu tsaro babu abin da zai yiwu." Buhari ya ce.
Najeriya ta kwashe fiye da shekaru shida dai ta na fama da hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram wacce ke ta da kayar ba a arewa maso gabashin kasar da ma wasu makwabtan Najeriyar kamar su Chadi da Nijar da Kamaru.
Kuma a lokacin ranstar da Buhari da ma ya sha alwashin kawar da kungiyar inda ya nemi cibiyar tsaron kasar da ta koma Maiduguri.
Ziyarar Kasashen Ketare
Game da batuan ziyayar kasashen ketare da ya kai tun bayan da ya hau karagar mulki, lamarin da wasu ke cewa yana yawo da yawa, shugaba Buhari ya ce ya zama dole ya nuna godiya ga kasashen da suka taimakawa kasarsa wajen yaki da ‘yan ta’adda.
“Zuwa in godewa makwabtanmu da suka shigo har cikin kasarmu suka taya mu fada da ‘yan ta’adda za a ce wani abu? ko kuwa idan aka gayyace ni manyan kasashen masu arziki wadanda suna so su taimake mu, suna so su ji daga bakina wane irin taimako mu ke so ai ba tafiyar banza ba ce.” Buhari ya ce.
Game da tafiyar da ya je Afrika ta Kudu inda za a yi taron kasashen Afrika na AU, Buhari ya ce tun da shi sabo ne akwai bukatar ya je ya ga yadda ake gudanar da taron a matsayin na sabon shugaban Najeriya.
Title :
Rashin Aikin Yi Ga Matasa Babbar Matsala Ce – Buhari
Description : Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce rashin aikin yi ga matasa a kasar babbar matsala ce idan aka yi la’akkari da cewa fiye da rabin a...
Rating :
5