*Ba Sa Cika Salloli Biyar
*Suna Baiwa Bako Aron Matansu
Duk da kokarin da gwamnatin Nijeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita kamar su Nijar, Kamarun, Chadi da sauransu suke wajen ganin sun murkushe kungiyar Boko Haram, kwatsam sai ga shi wata kungiya makamanci haka na neman bullowa a jihar Kebbi, inda ake yi musu lakabi da ‘Yanlabbaika.
Har zuwa yanzu dai ba a zargi kungiyar da tayar da wata tarzoma ba, sannan kuma suna gudanar da wa’azi da taro a ne a iya yankunan da suke.
Sai dai bincike ya nuna cewa daga cikin akidojin ‘yan kungiyar wadanda ake kuma yi musu lakabi da ‘Yanlokoloko, gudanar da salloli biyar din da Musulunci ya shar’anta ba ya daga cikin tsarin su, sannan kuma a duk lokacin da suka yi bako su kan ba shi aron matar su ya kwana da ita.
musamman idan bakon babban malami ne a akidar ta su.
Sannan kuma binciken ya nuna cewa suna fifita jagoransu fiye da Allahn da ya halicce su.
Wata majiya ta rawaito cewa shugabannin kungiyar suna daga cikin wata kungiya makamancin haka da aka kora daga jihar Neja,
inda wasu daga cikin shugabanninta suka sauya sheka zuwa jihohin Borno, Yobe, yayin da wasu kuma suka yi kaura zuwa jamhuriyar Nijar.
A yayin da manema labarai suka ziyarci masallacinsu da ke kusa da ofishin wutar lantarki, sun tarar da wasu mabiya kungiyar zaune a bakin masallacin.
Wani mazaunin unguwar ya ce, a wasu lokutan mabiya kungiyar su kan yi salloli biyu ne a yayin kowace rana tare da cewa Shehi zai karasa musu sauran guda ukun.
Kuma su kan yi raka’a biyu ne a sallolin da ke da raka’o’i hudu.
A ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu da wasu mazauna yankin suka yi, sun nuna cewa mabiya kungiyar sukan yawaita zama ne a kofar gidan wani mai suna Malam Labarasi da ke unguwar Gwadangwaji.
Da yawa daga cikin mu ba ma sallah a masallaacin su.
Ba mu ma damu da harkokinsu ba, har sai lokacin da muka soma ganin manema labarai suna zuwa don yi musu tambayoyi, ba mu san da zaman su ba ma”, kamar yadda wani mazaunin yankin ya ce.
Bincike ya nuna cewa kungiyar ta kafu ne tun shekaru sha biyar da suka gabata, sannan kuma suna da mabiya da dama, a jihar ta Kebbi duk da cewa da yawa daga cikin membobin kungiyar suna fita su bar ta bayan sun gano alkiblar da ta dosa.
A yayin jin ta bakin Dagacin garin na Gwadangwaji, Alhaji Umar Ahmed, ya musanta batun cewa akwai kungiya makamancin haka.
Sannan kuma ya kara da cewa a matsayin sa na shugaban al’umma idan abu makamancin haka na faruwa, ba ‘yan jaridu zai yi hira da su ba, gwamnati ya kamata ya sanarwa.
A gefe daya kuma, a yayin jin ta bakin mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Sama’ila Dabai Yombe game da lamarin, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na kan gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an tsaro suna kan binciken lamarin.
Sai dai ita ma rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa har zuwa yanzu ba ta da labarin wadannan mutane, kamar yadda mai magana da yawun rundunar ASP Nafi’u Abubakar ya bayyanawa majiyarmu ta waya, inda ya kara da cewa za su gudanar da bincike da zarar rahoton ya iso gare su.