Bakamin artabu sukaiba sannan ta fahince shi amma dukda haka sam hankalinta yaki kwanciya gani take ancuceni sannan anzalinceni tana bala in kaunata batason abinda zai cutar dani
cikin sati daya magana ta kankama batare dana saniba umma dukta rame bata da aiki saina kuka kamar yarinya nai tambayar harna gaji amma taki cemin komai
dawowata kenan daga makaranta sallamata uku amma ba amsa kauri naji na nufi kichin ga umma zaune amma miyarta ta kone sabida tsabar tunani nasauke miyar sannan nasa kuka me tsanani ummata rude takama aikin lallashina zuwa dare
nalallaba na dauki wayarta na dauki nomber din ya Aliyu domin banida ita kuma nasan shine matsalar ummana sai karfe goma na dare sannan na kira dukda kirjina yanata faman bugawa bantaba yin waya dashiba tajima tana ring sannan ya daga dayin sallama
na amsa cikin sanyin muryata tare da gaisheshi ya amsa yanajin dadin muryar besan kotawaceba
nace ya Aliyu rahmace dan Allah inaso inyi magana dakai inban takurakaba
cikin isa yace inajinki nace kayi hakuri kaimin alkawarin bazaka kashe wayarba yace nayi lfy ko
nace gaskiya nagaji daganin kukan umma batada matsala saitaka kullun kuka kullun kuka kana tunanin Allah zaibarka kullun mahaifiyarka tana zubar da hawaye kanka
wlh kayi rashin wayau da tunani duk ilminka yatashi abanza rabon daka hada ido da umma harka manta kaji kunya kuma kayi asara kafita hanyar umma tunda bakasonta mu muna sonta bamushirya maraiciba malan angirma ba asan angirmaba naitsaki tare da kashe wayar ina maida nunfashi
lamo yayi yana sauke ajiyar zuciya muryata kawai kemai kuwwa akunne
wata nadama ta saukarmishi yana mamakin tsiwata yake. jiyai yanason ya ganni yatuna rabondaya ganni harya manta.
Ranar juma.a aka daura aurena da ya Aliyu
kwance nake tunda nadawo mkrt marata tanamintsami da ciwo naji hayaniya falo na nufa naji muryar mamee tana Allah ya yadda yau andaura auren rahma da Aliyu Allah yakawo zuri ah masu albarka namaida kallona kan ummah tai tagumi tana ta faman hawaye
tabbas gaskene wani duhu ya mamaye ganina daganan ban kuma sanin komaiba
Saidai daf da magruba nadawo hayyacina abba shine mutun nafarko dana hada ido da shi naisaurin rufe idon ina hawaye jinake kamar inhadiyi zuciyata na mutu kona huta baba yashigo da likitan yana yimai bayanin ta farka drif din yaciremin tareda. jeromin tambayoyi amma ban amsa kodayaba dole yace sufta subarni na huta tukunnah
umma kadai taki fita rungumeni tayi tana hawaye sai yanzu nagano abinda yahanata kwanciyar hankali cikin kwanakinnan
tace kiyi hakuri narasa yanda zanyine amma zansa yarabu dake babu wanda zaitaku ramiki
kwana biyu aka sallameni kowa lallashina yake da daddare abba ya aiko direba yana son ganina naima umma sallama nafita tana kara gayamin bata yadda inkwanaba jikin abba nakwanta ina shakar kamshi ya mamee tai dariya rahma yaushie zaki girmane
nace mamee haka zan zauna bazan girmaba abba yace abindayasa nakiraki shine domin inkara baki hakuri akan hukuncin damuka yanke batare da jinta bakin kiba kiyi hakuri rahma kijure kodan ummanki tarikeki da amana badata taba bata mikiba kidaure kiyi wannan jahadin domin jahadi zakiyi rahma
yayan naki yananan zuwa gobe keya kamata ki lallashi umman taki domin haryanzu taki warwarewa kadda kiyarda kinuna mata bakiso kinji insha
Allahu zakuji dadi nan gaba
mamee ma tadora nata nasihar tashigeni
sosai kuka nake sosai abba yana lallashina rubutu yabani galan biyu yace intasha zaimin bayani daga baya sannan yasa amaidani gida
agajiye nadawo daga makarata umma taimin sannu nanufi dakina domn watsa ruwa kwance naga mutun kan gadona yayi daidai yana kwasar barci abinshi lokaci daya tsoro ya mamaye zuciyata dana tuna abba yagaya min yau ya Aliyu zaidawo wajan umma na nufa nace umma mutun kan gadona
tadan tabe baki tare dacewa yayankine ya dawo dazu ba ashare dakinshiba shine yace zai huta kamin agyaramai
cikin sanyin jiki nanufi dakin zucciyata tana min wani zafi tsanar ya Aliyu tana kara kwarara cikin zuciyata jinake kamar na yankashi wlh
toilet kawai na shige nai wanka tare da dauro alwala dagani sai daurin kirji nagama abinda zanyi sannan nai sallah ashe yatashi kallona kawai yake ina juyawa muka hada ido naharareshi nace wannan kallon duk na maye nidai wlh nan gani nan bari
nabar dakin jikina yana rawa domin ninasan waye kaftin Aliyu
mamaki yai matukar kamashi ranshi ya baci lallai yakamata ya koyama yarinyarnan hankali dukda cewar yana son tsiwaddanake da ita kumafa kallanda yaimin ya tasoda sha awarshi dole yafita domin biyan bukatarshi tunaninshi daya su baba sun rainashi da zasu auramai wannan kwailar yarinyar mezaiji jikinta
yana sa manyan yan bariki kuka inaga wannan tsaddar yar saidai konan gaba inta girma domin yaga akwai kaya ko yanzu balle inta karawayau