PDP, ta shirya yin adawar da ba’a taba yin ba a tarihin Najeriya, Sanata Abubakar Gire, ne ya furta haka a wata hira da wakilin muryar Amurka Hassan Maina KainBuharia, a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Yace PDP, zata yin adawa bisa ga ka’ida da mutunci bisa ga tabbatar da cewa Gwamnati na kowa ne fatar su shine a shekarar 2019, mulki ya koma hannun PDP.
Sai dai a daidai lokacin da ‘yan PDP. Ke shiryawa adawa bisa dukkan alamu Jamiyyar tasu ta shiga rudani.
Cif Tony Aneneh dake Zaman shugaban kwamitin amintattun jamiyyar ta PDP, yayi murabus a ‘yan kwanakin nan ya kuma ce yayi hakkan ne domin baiwa Goodluck Jonathan, damar darewa bisan kan wannan mukami, amma Goodluck yace a kai kasuwa.
Dr. Umar Ardo, wani jigo a jamiyyar ta PDP, wanda tun farko yayi adawa da yin takarar Goodluck Jonathan, wanda kuma suka tafka sharia har zuwa kotun kolin Najeriya, yace Cif. Tony Aneneh, ya sauka daga kan mukamin don dole ne ba dan yana so ba.
Title :
PDP ta Shirya yin Adawa da Gwamnatin Buhari
Description : PDP, ta shirya yin adawar da ba’a taba yin ba a tarihin Najeriya, Sanata Abubakar Gire, ne ya furta haka a wata hira da wakilin muryar Amurk...
Rating :
5