DAGUDU TAKARASA cikin gidansu tana murna afalo ummanta tatareta tana tambayarta komeke faruwa naganki cikin farin ciki haka.
:
Shakira tay saurin dawowa cikin hayyacinta ta tunafa ita soyayyar sirri takeyi domin batason mahaifanta su san cewa takamu dason wani tunda mas ud sudai suke so ta aura.
:
Koda tayi wannan tunanin saita dubi ummannata tace bakomai umma kawai ganinai birthday dina yakusa zuwane shiyasa nake farin ciki dazuwansa.
:
Umman tayi murmushi tace idanma baki fadi gsky badai idan tayi tsami maji.
:
Dakinta shakiran tawuce tana zuwa tafada kan gado takama tsalle waini yau dantala ya aiko yace yana sona wayyo Allah yau ina zan saka kainane tazaro waya numban zahra talalubo.
Aikuwa bata jima tana ringin ba zahran tadauka tace hello kawata ya akai ne.
:
Shakiran tace cikin farin ciki zahra kinga planing dinmu yayi domin dantala ya aiko babban abokinsa dasako yana sona dazu dazunnan bayan mun rabu dake.
:
Zahra ta fashe da dariya tace tokingani yanzu duk wata matsala takau danhaka yanzu saiku fara sharbar soyayya koya kikace yar uwa.
:
Kedai bari kawata saima kingani da idonki.
A ah nifa banason azarbabi dayawa jan ajinnan naki nakeso kici gabadayimashi dan bazaiyiwu shikenan dan yace yanasonki kuma saiya sameki asaukiba.
:
Zahran ce tai wannan furucin.
Ke zahra bakida hankali idan naja masa aji yakwacefa ke kinsan yadda nakeji da dantala acikin zuciyata kuwa, shifa kamar danyan kwaine wanda kodayaushe yake cikin riritawa agareni.
:
Amma am sorry pls zanja aji amma dai yadda kwakwalwatrsa zata iya dauka ko?
:
Tatambayi zahra.
Kekika sani nidai shawara nabaki kawai inji zahra sannan takashe wayar bata ko saurari abinda shakiran zata ce mataba.
:
Shakira tai dariya sannan tacire wayan daga kunnanta.
Kash abinka da rashin sani ashe tundazu datake waya mahaifiyarta tadade da shigowa cikin dakin tanajin abinda suke tattaunawa da zahra sannan agabanta duk tafadi komai.
Shakiran na waiwayawa bayanta saitaga ummannata a tsaye kawai tana kallonta.
:
Alamar mamaki da razana suka bayyana karara daga fiskar shakira tace umma....
Bata batta tace wani abuba sannan tace mata.
Ni shawara zanbaki shakira kedai 'yatace guda daya wacce nahaifa ko?
Shakira Tagida kai.
To ina baki shawara kicire son wannan dantalan danaji kina ambata awaya dan babanki da baban mas ud saurayinki sun zauna sunyi maganar aure rana kawai ake tsimayi a tsayar miki.
:
Sannan zan miki adalchi bazan fadawa abbankiba kiyi kokari kicire sonsa daga zuciyarki
kodan ki kasance cikin kwanciyar hankali taredamu gaba daya.
:
Tana gama maganar tajuya tafice daga dakin.
:
Wasu hawayene suka zubo daga idanun shakira, tace acikin zuciyarta tab gsky ayanzu mai rabani da dantala tofa indai ba mutuwaba saidai wani ikon Allan.
:
Babu kalmar da shakira tatsana arayuwar irin taji ance tarabu da dantala hakika inbadan wadanda suke bata shawarar hakanba ma abota kusanci da itane sosai da babu yadda za ai bata cimusu mutunciba koda suwaye.
:
Allah sarki sofa kenan wanda zaisa kabijirewa kowa kayi biyayya ga abin kaunarka/ki.
*******
sunanta shakira 'yar gidan alhaji abbas ce wani shahararren dan kasuwa mai cin gashin kansa.
:
Gidansu yana kundila layi na uku numbar gidan itace 94.
:
Wannan itace sallamar da sale yayiwa dantala bayan sun rabuda shakira abisa sakon dayace dantala ya aikoshi sannan yakoma wajen 'yan aikin inda yasamu dan talan shi kadai yana jiransa azaune.
Dantala yajuyo dasauri yadubi sale yace naji to amma ya labarin sakon soyayyar dakakaimata danni wlh hankalina atashe yake sabida na matsu naji sakamakona.
Dantala yai dariya yace nafada mata sakonka ammafa gsky....
Amma me? Dantala yakatseshi
amma batasona ko.
Shikenan dama nasani ai babban goro sai magogin karfe.
Sale yai dariya yace aikai matsalarka kenan dantala yanzu bangama jawabiba kawai kakama ka katseni a ah.
Dantala nasami shakira nafada mata sakonka sannan tayi farinciki tace tana maraba dakai cikin aminci ma ana dai takarbi sakon soyayyarka.
Wani farin ciki ya lullube dantala sannan ya rungume sale tared a yimasa gdy.
Sannan yakalleshi yace idan kuwa hakane Allah yakaimu gobe dan saina kara jaddadada soda kauna idan sukazo gurinmu.
:
Insha Allahu bazan barta tatafiba saimunyi hira irinta ma abota soyayya.
Sale yace yawwa hakanakesonka namiji yanzudai ina kudin aikina.
Dantala yazara masasu yabashi gamida ture masakai yace zan hanakane.
:
Sale yakirga yaga sun cika cif sannan yakara duban dantala yace ina kuma kudin aiken dakaimin.
:
Dantala yai murmushi yace waikai bakada imanine sale wai ina zakakai kudine.
:
Kaga dan Allah zomu tafi magribafa takusa gabadaya sukai dariya suka tashi daga wajen.
:
Aranar gabadaya dantala afarinciki yakwana ita kanta mahaifiyarta da taga dantala yajuye mata da kuma taga nutsuwarta tadawo yau daya saida abin yabata mamaki sannan tai godiya ga Allah...
:
Afuwa zan ci gaba gobe
yi comment dan nuna ra ayinku Muna Bukatar 100 Comment..
:
Just Comment Below...