HABA SHAKIRA yanzu kinanufin bazaki kara rakani zuwa gurin 'yan aikinnanba kenan?
Zahra ce tai furucin lokacin datasauke shakiran daga mota suke kokarin yin bankwana.
Shakira tai murmushi tace to meye abin damuwa kawata tunda abindanake zuwa dominshi dama nariga nasamu sannan kema ai ba wani abin tashin hankalibane agurinki tunda saura kwana 2 fa kawai asallami su manaja daga asibiti kema kinga basaiya karbeki kihutaba.
:
Zahra tace eh duk dahaka ammadai kingani ai bansababa zuwa gurinnan nikadaiba ko.
Shakira tai murmushi akaro nabiyu sannan tace yanzu saiki saba dama ai nadade ina neman irin wannan ranar dazakije gurinsu ke kadai sannan ki sallamesu kekadai takarasa maganar cikin karamar dariya sannan tace kingama gobe nagayyaci dantala zuwa gida musha hirar mu ta soyayya kekuwa kina gurin 'yan aiki.
Mamaki ya bayyana afiskar zahra tace ke shakira naga alamar dai bakida hankali shiyasa harkika gayyaci dantala xuwa gidanku shin kin manta da mas ud ne saurayinki wanda ake niyyar saka muku rana kodayaushe,
sannan kinahauka ne da abbanki zai barki ki dinga soyayya dawani bayan mas ud kuma kinsan akwai yarjejeniyar aure a tsakanin iyayanki danashi.
Shakira tai dariya sannan tace kinga saki ranki abbadai yayi tafiya yana ghana kuma bazai dawoba sai yayi wata daya complete.
Sabida kinsan karfin kasuwancinsa acan yake.
Sannan danta umma karki damu ayau zan nemi alfarma agareta nasan umma akwai sanyi sannan tana sona sosai danhaka bazata so abinda zai batamin raiba kokadan kinga daga nagama da wannan pressure sai kawai muyita shan soyayyarmu nida masoyina ko yakika gani.
Zahra tace hakane amma shakira soyayyarki da dantala tana bani tsoro sabida koyaushe sainaga kamar akwai abindazai iya kawomuku cikas acikin lamarinku.
Koma mainene baifin karfin ubangiji inji shakira.
Zahra tace hakane.
Sabida haka karki damu kawata kisaka ranki a inuwa insha Allahu banida miji sai dantala kuma nariga nayi rokon Allah yazama mafi alkairi agareni.
Ahakadai sukayi sallama ita zahra nakokarin tafahimtar da shakira matsalolin soyayyarsu ita kuma shakira tanayimata nunin babu komai.
******
Azaune suke akan dining table din suna break fast sukadai agidan
shakira tadubi mahaifiyarta tai murmushi tace umma.
Ta amsa na am.
Tace arayuwata tunda nataso duk abubuwan dana ce inaso koke kokuma abbana kunayiminshi sannan bana yabon kaina iya biyayya daidai gwargwado da da yakewa mahaifansa nasan ina kwatantawa
umma ina kaunarki dan kaunar dakikemin dakuma sanki da Annabi s a w na rokeki alfarma gudaya kozakimin ita.
Umman shakira tai shiru jin wannan kalaman daga bakin 'yar ta hakika kalaman su ratsata sosai sannan sunsakata nutsuwa na lokaci nan take datajisu.
Danhaka tadago dakai tadubi 'yar tata shakira tace fadi bukatarki 'yata komai nene in Allah yaso ya amince saina biya miki ita inhar zan iya.
Shakira tadan maida numfashi sannan tace umma basaina fadamaba ke kanki kinsani kokadan banason mas ud wanda akeso a auraminshi sannan nasani tun ina karama kuke alfahari kuganni acikin farinciki danhaka umma dan Allah kubarni na auri wanda raina yakeso.
Umma dan Allah kifahimtar da Abba sabida yanada zafi idan ke kin fiskanceni shiba lallaine ya fiskanceni.
Umman tadubi shakira tace wayeshi wanda kikeso din.
Tace dantala.
Waye kuma dantala aina shi yake.
Shakiran tace gobe zaizo nagayyaceshi gidannan amma kafinnan inason ki taymakamin da goyan bayan soyayyarshi dan wlh shi nakeso umma banason mas ud.
Dangane da halayyarsa kuwa nabaki dama kiyi binciki inhar kika binciko wani baki daga gareshi to na amince yazama makami naraba nidashi har cikin zuciyata.
Sannan umman tanisa tace inason farin cikinki shakira sabida haka inason abinda kikeso amma matsalar itace abbanki duk dahaka zanyimiki kokari na fahimtardashi duk dacewa yin hakan zai wahala.
Yawwa umma dan Allah kitaymakeni umma kinji shakiran tace
karki damu in Allah yayarda idan yadawo daga inda yatafi zanyi kokari na fahimtar dashi.
Yawwa umma nagode Allah yasaka da alkairi
*****
wani wankan fara shadda yai maiky yau tayimasa kyau kuwa matuka dayake dama kyakykyawane yasami wata farar hula wacce tadace dakayan ya dorata akansa idan kaganshi inbadan kasanshi kuma kasan daga wanne gida yafitoba saikai masa kallon dangidan wani hamshakin wani mai kudinne.
Duk dacewa yau yasaka niyyar zuwa gurin shakiran baiki zuwa gurin aikiba saidai ana sallar la asar yabar gurin bayan yabawa sale sako cewa yakarbar masa kudin aikinsa idan ankawo shi zaije wajen sahibarsa.
Adaidata sahu yahau dayake bashida wani abin hawa sai wani tsohon kekensa wanda yamadade da lalacewa sannan yakaraso inda gidan yake.
Yakalli gidan sosai tawani bangaren kuma saigidan yadingayimasa kwarjini shin yashigane kodai karya shiga .
Anya kuwa shakira anan take?
Dukdacewa adress din da sale yabashi yayi daidai danunin gidan dayazo..
:
Afuwa zancigaba
yi comment dan nuna ra ayinku Yanzu...send Next Part 11...