Mutane akalla 23 ne suka rasu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a N'djemena babban birnin kasar Chadi.
Lamarin kuma ya janyo jikkatar mutane fiye da 100.
Shaidu sun ce 'yan kunar bakin waken sun zo ne a kan babur kafin su tayar da bam a lokaci guda a wajen shalkwatar 'yan sanda da kuma cibiyar horas da 'yan sanda.
Tuni aka aika dakaru zuwa yankin domin kwantar da kura.
Dakarun Chadi na taka muhimmiyar rawa a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta addabi Nigeria da Nijar da kuma Kamaru.
A wata mai zuwa rundunar hadin gwiwa domin yaki da Boko Haram za ta soma aiki inda shalkwatarta za ta kasance a N'djamena.