Mutane 18 ne suka mutu sakamkon wata arangama da aka yi da 'yan sanda da kuma Musulman Uygur da aka hana azumi a makarantu da ofisoshin gwamnati dake kasar China.
'Yan sandan na China sun ce mutanen Uygur din sun kai musu hari da wukake da abubuwan fashewa.
'Yan sandan sun kuma ce an kashe musu akalla jami'ai uku.
A sanarwar da aka fitar an bayyana cewa an kashe mutane 15 a fafatawar da aka yi tsakanin 'yan sanda da sauran mutanen.
Title :
Musulman China da aka hana azumi sun fafata da 'yan sanda
Description : Mutane 18 ne suka mutu sakamkon wata arangama da aka yi da 'yan sanda da kuma Musulman Uygur da aka hana azumi a makarantu da ofisoshin ...
Rating :
5