Mayakan IS sun yi awan gaba da wasu lilamam Masallaci a arewacin iraki Wadanda suka ganewa idanunsu abinda ya wakana sun bayyana a wannan Assabar mayakan kungiyar ta’addanci IS ko da’esh a takaice sun killace wasu massalatan birnin Mosil, sannan suka yi awan gaba da limaman masatan. Daga cikin limaman da aka yi awan gaba da su a kwai Limaman Masalatan Azahra, Almufty, Almakhyul, Aliyu bn Abi Talib da kuma Muntasurulla… A ranar juma’ar da ta gabata, kungiyar ta IS ta sanar da cewa Sallar Tarawuhi jam’u a cikin masalatai bidi’a ce ,kuma duk limamin da ya jagoranci wannan salla a masalatinsa zai fuskanci hukunci, lamarin da wasu ‘yan garin na Mosil ke ganin cewa kamun da a ka yiwa limaman ba ya rasa nasaba da wannan sanarwa.
A bangare guda kuma dakarun kasar Iraki na ci gaba da kai hare-hare ta sama a kasa domin tsarkaka kasar daga mayakan kungiyar ta IS, inda a jiya ma jiragen yakin kasar suka kai hare-hare kan mabiyar ‘yan ta’addar na IS a yankin Falluja tare da hallaka biyar daga cikinsu.