Assalamun 'alaikum. Da fatan malan yana cikin koshin lafiya tare da zuriyarsa gaba daya, Allah Ya sa haka amin, Allah Ya jikan mahaifa da malamai amin. Malan don Allah taimako nake nema, yaro na ne dan shekara goma sha uku a yanzu haka, amma tunda ya kai shekara sha daya wasu lokuta da dama azakarinsa a tsaye yake ko da bacci yakeyi, an tambaye shi meyekeyi da kullum yake kasance haka? ko yana mafarki? yace baya komai, kuma baya mafarki, shi ma dai haka yake ganinsa, kuma ko waya babu a hannusa balle ayi tunanin ko yana kallo abinda bai kamataba, bisa ga dukan alamu shima abin yana damunsa, shine nake so don Allah ka tamaimake mu da shawara ko magani in akwai. Daga dalibar zauren fiqhu. Don Allah aboye Id dina.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Irin wannan matsalar tana da dalilai da musabbabai da dama. Domin kuwa alokacin da Dan Adam Namiji ko Mace shekarunsa suka haura goma, to sinadarn kwayoyin halittar jikinsa sukan fuskanci wasu chanje chanje, saboda kusantowar balagarsa.
Abinda zakuyi shine ku garzaya dashi wajen Babban Likitan Ilimin Halittar Dan Adam (Gynaecologist) ya dubashi ya baku magunguna.
Bayan nan kuma zai yi kyau ku kaishi Cibiyar Lafiya ta Musulunci (Islamic Health Centers) mafi kusa domin ayi masa rukyah.
Abinda yasa nace haka, wani lokacin JINNIYYATUL ASHIQAH (ALJANAR SOYAYYA) ta kan auri yaro namiji tun kafin ya balaga. Kuma tun sannan zata rika zuwa masa a mafarki tana saduwa dashi.
Daga cikin magungunan da zaku yi amfani dasu
1. Ganyen Na'a na'a wanda aka chakudashi da Lubban Zakar. yana kwantar da hankali, kuma yana daidaita tafiyar jinin jikin Dan Adam. Kuma yana Wanke kwakwalwar mutum.
Ku rika dafawa yana sha ba tare da madara ba.
2. Idan akwai alamar shafar Aljanu tare dashi, to ku nemi MUHRIQUL JINNI da kuma ALMUJARRAB na ZAUREN FIQHU kuyi amfani dashi. in dai Aljanah ce ajikinsa to zata Qone, kuma zata rabu dashi da yardar Allah.
Allah ya sawwake.
WALLAHU A'ALAM.