TAMBAYA TA 1623
*******************
ASSALAMU ALAIKUM Malam aranar 28 FEBRUARY 2014 kayi maganar za a hada Tambayoyin ZAUREN FIQHU Guda 1000 za a mai dasu littafi. Malam ko Allah yasa anyi?.
Sannan kace za a fitar da Application na Android wanda zai kunshi tambaya da Answer ko sun samu?
TAMBAYA 1-Yarinya ce budurwa take fama da ciwon mara. Malam sunje Asibiti abin yaci tura kuma bata mafarkin komai kuma babu abinda ke fita agabanta. ciwo kawai takeji. Malam Dan Allah ataimaka mata da abin da ya dace.
TABAYATA 2-YARO ne aka aka haifa shekara guda da wata shidda. ko zama bai iya ba an nemi magani abin har yanzu. Malam dan Allah idan akwai abin taimakawa a taimaka. IDAN kuna da branch a ZAMFARA sai aban address. Nagode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Na karanta Wasikarka kuma na fahimci dukkan sakon da take kunshe dashi.
1. Rashin yin mafarki bq shine hujjar cewa babu aljani ajikinta ba. Kuma akwai bukatar sanin cewa Shin ciwon marar yana zuwa mata ne alokacin da zatayi jinin Haila, ko kuwa awani lokacin ne daban??
Amma ku samu ganyen lalle, ajikashi tare da tsamiya. Idan ya jika sai arika sha. (amma ban da mai juna biyu) insha Allahu ciwon marar zai dena.
Shi kuma yaron arika dafa masa garin hulba cokali guda idan ya dahu sai asanya zuma sannan arika bashi yana sha.
Sannan ku samu Man Zaitun mai kyau ku karanta ayatushi shifa'i acikinsa tare da Qul HUWALLAHU, falaki da Naasi Qafa uku uku. Sannan arika shafa masa. Kuma ana bashi yana sha.
BAYANI AKAN LITTAFIN ZAUREN FIQHU :
Muna nan acikin aikinsa, mun fito dashi daga Internet, Mun rubutashi ajikin takardu, kuma yanzu haka muna nan mun kafa wani kwamiti na Malamai wadanda suke taimaka mana wajen gyare-gyare acikin aikin.
Kuma in sha Allahu acikin shekarar nan ta bana, littafin zai fito.
Kuma muna godiya sosai abisa damuwarku da kuma kulawarku akan sha'anin ZAUREN FIQHU. Allah ya saka muku da alkhairi.