Majalisar malamai da Limami ta jihar Kaduna ta ce ta yi mamakin jin matakin da gwamnatin jihar ta dauka na soke ciyarda marasa karfi a lokacin azumi da aka saba gani ana yi shekara shekara
Sheikh Abubakar Usman Baban-Tune , shugaban majalisar Limamai da malamai a Kaduna, ya bayyana matakin a matsayin wata gurguwar dabara.
'Alal hakika ana tausaya bayin Allah, kuma ana jinkan bayin Allah a cikin wannan watan' in ji Sheikh Abubakar.
Ya kara da cewa 'akwai wadanda suke da rauni'
Gwamnatin jihar dai ta ce ta yi hakan ne don rage facaka da kudaden gwamnati, kuma a cewarta mutane kalilan ne ke amfana da tallafin.