MALIK BN DINAAR (RAH) yana daga cikin magabata na kwarai. Watarana wani barawo ya shiga gidansa domin yin sata, Barawon ya bincika bai samu komai ba.
Ashe Malik din yana kallonsa. Har barawon ya juya zai fita sai ya kirashi yace masa "TUNDA KA SHIGO KA DUBA BAKA SAMU ABIN DUNIYA BA, SHIN KANA SO MU BAKA NA LAHIRA?".
Sai barawon yace masa "Eh". Sai yace masa to Ga ruwa nan ka tashi kayi alwala kayi sallar Nafila raka'a biyu..
Bayan barawon ya kammala nafilar, sai suka zauna tare, yana yi masa wa'azi har zuwa lokacin Sallar Asubah.
Da mutane suka gansu tare a Masallaci sai suka tambayi Malik (rah) "Mai ya hadaka da wannan mutumin?".
Sai yace "YAZO ZAI MIN SATA NE, NI KUMA SAI NA SACHE SHI"...
DARASI
*********
Wannan labarin yana katantar damu cewa Ka zama Mai Janyowa Zukatan Mutane zuwa ga Mahaliccinsu. Kar ka zama mai korar mutane ta hanyar Kafirtasu ko Muzantasu, ko Zaginsu da bakaken maganganu.
Idan ka gansu suna aikata wani zunubi, ko wata bidi'a ne, ko kuma wani abinda kai baka fahimta ba, to gara ka zauna dasu cikin hikima ka saurari Hujjojinsu (In har suna da hujjar) Idan kuma basu da hujjar, ko kuma Hujjar tasu ba mai karfi bace, sai ka gindaya musu naka Hujjojin tare da kiransu zuwa ga hanyar Allah cikin hikima.
Idan kuma ka tsaya Kafirta Musulmai ko zaginsu da bakaken maganganu, to wallahi laifinka yafi nasu Muni. Domin kuwa zagin musulmi fasikanci ne.
Ubangiji yana murna da bayinsa masu kokari shiryar da wadansu.. Kuma yana fushi da bayinsa masu kore masa wasu bayin daga kan hanyar Shiriya.
ZAUREN FIQHU