Dan kwallon Cheslea, Gael Kakuta ya koma kungiyar Sevilla ta Spain.
Kakuta mai shekaru 23, ya koma Stamford Bridge daga Lens a shekara ta 2007 amma ya shafe kakar wasan da ta wuce a matsayin aro a Rayo Vallecano.
Dan kwallon Faransa din ya buga wa Chelsea wasanni sau 16 sannan ya tafi aro a kungiyoyi daban-daban shida.
A shekara ta 2009, Chelsea ta shiga cece-kuce game da sayen Kakuta daga Lens inda sai da aka shiga gaban kuliya kan batun.
Title :
Kakuta ya koma Sevilla
Description : Dan kwallon Cheslea, Gael Kakuta ya koma kungiyar Sevilla ta Spain. Kakuta mai shekaru 23, ya koma Stamford Bridge daga Lens a shekara ta 2...
Rating :
5