TAMBAYA TA 1632
********************
Assalamu alaikum Dan Allah Malam a taimaka min da shawara ko addua Ni na kasance matar aurene a da. kaddara ta sa na rabu da mijina Amman Yanzu mun shirya a tsakanin mu na yafe masa abinda ya min Amman iyayena sun ki su barni na koma asalima suka kiran a gefe suka ce idan har na koma to wallahi bani basu har abada saboda irin wulakancin da yamin a baya. Malam a taimakamin da shawara wallahi duk mutanen da suka fito neman aurena basu kwanta min a raina ba kamar mijina na da ba. Daga wata baiwar Allah. Hide my identity please.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah. Gaskiya kina cikin tsaka mai Wuya. Musamman idan an dubi irin soyayyar da taje tsakanin Mutanen da suka taba zama tare amatsayin Ma'aurata.
Amma Hukunci anan shine KIJI TSORON ALLAH KI BI MAGANAR IYAYENKI. Domin hakkin iyaye akan 'Ya'yansu ba Qarami bane. Allah ya riga ya wajabta mana bin iyaye acikin dukkan abinda babu sabon Allah cikinsa.
Da ace kinyi yaji ne, ba wai rabuwar aure ba, to anan dole Maganar Mijinki ita zaki bi. Amma tunda ya sakeki har kin gama iddah, to babu damar yi nasa biyayya kamar tun farko.
Kuma shawarar da zan baki ita ce: Ki gaya masa yaje da kansa ya samu iyayenki ya basu hakuri, ya nuna musu cewa ya amsa laifinsa kuma ba zai Qara ba. Watakil hakan zai sa su huce su yarda a mayar muku da auren.
Ya kamata Ma'aurata su rika hakuri da juna. bai kamata ju rika daukar kowacce magana kuna gaya ma iyayenku ba. Zata yuwu daga baya ku shirya da junanku, alhali su kuma iyayenku basu huce ba.
Allah ya kiyaye, Allah ya gyara lamarin.
WALLAHU A'ALAM.