TAMBAYA TA 1638
*********************
Assalamu alaikum. Allah shi gafarta Malam mainene hukuncin Musulmin da yake sayar da Sarkoki ko kayan ado wadanda suke dauke da alamomin addinin da ba na Musulunci ba? Shin ya halatta ne, ko bai halatta ba??
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah. Bai halatta musulmi ya rika sayar da duk wani abinda yake dauke da wata alamar wani addinin daban ba.
Misalin sarkokin nan masu dauke da Kuros (CROSS) ko kuma rigunan da suke dauke da alamomin addinin Yahudanci.
Yin hakan kamar taimakawa ne cikin aikata sabon Allah. Alhali kuma Allah yana cewa: "KUYI TAIMAKON JUNA BISA BIN ALLAH DA TAQAWA, AMMA KAR KUYI TAIMAKON JUNA CIKIN SA'BON ALLAH DA KUMA QETARE IYAKA".
(Ma'idah ayah ta 3).
WALLAHU A'ALAM.