TAMBAYA TA 1643
*********************
Assalamu alaikumu wa rahmatullah... malam don Allah mace ce take al'ada kwana 6, To dama kafin yazo sai da wani discharge kamar bounvita tsinkakke ya fara zuwa, aka ce mata shima period ne, ta dakata da azumi da sallah, bayan kwana1 da haka jinin yazo sosai, har dai tayi kwana 6 data saba. bayan ta duba da audunga taga white discharge daga nan tayi tsarki taci gaba da ibadah. sai da taje fitsari sai ta kuma sanya cotton can sai taga wannan discharge din mai kamar bounvita amma bai kai ma duhun bounvita ba ya dawo, kuma ko a pant dinta bai digo ba, shine take tambaya don Allah ya ibadarta zai kasance kenan? yanzu haka dai ta dau azumi ta karya ne ko kuwa? Don Allah malam ka taimaka mana da amsa. Allah ya saka maka da gidan aljanna.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh. Shi wannan ruwan mai kamar kalar Bounvita idan yazo bayan kin riga kinyi tsarki kinyi wanka, to BA'A LA'AKARI DASHI.
Kamar yadda hadisi yazo acikin Sahihul Bukhariy da Sunanu Abee Dawud daga Ummu 'Atiyyah (ra) - wato Nusaybah Bintu Ka'ab Al-Ansariyyah sahabiyar Manzon Allah (saww) tace:
"MUN KASANCE BAMU KIRGA GURBATACCEN JINI DA KUMA JAJA-JAJA AMATSAYIN WANI ABU - BAYAN MUN RIGA MUNYI TSARKI".
Imam San'aniy yace : Wannan JAJA-JAJA din tana nufin irin ruwan nan mai kama da kalar ruwan gyambo. Wato bassu daukar sa amatsayin wani abu ba. Wato ganinsa ba zai hanasu sallah ko azumi ba.
Kuma Imamul Bukhariy yace: "Wannan hadisin marfu'i ne kuma yana nufin cewa Taqriri ne daga Manzon Allah (saww) wato yasan da haka, amma bai ce komai ba. Don haka ya zama hujjah kenan.
Amma cewarta "BAYAN TSARKI" yana ishara ne zuwa ga cewar idan an ganshi kafin haila, to ana daukarsa ne amatsayin SHIMA HAILA NE.
Don haka kici gaba da azuminki da sallarki.
Don Qarin bayani aduba Subulus Salam Juzu'i na daya, acikin KITABUT TAHARAH, babul Haidhi.
WALLAHU A'ALAM.