Assalamu alaikum Malam da fatan ka wuni lafiya tare da iyalanka baki daya. Tambaya ce gareni dangane da Fatawar da ka amsa jiya.
Shin irin wadannan Matan da suke bada magani, idan suka yanka ma aljanunsu Kaza ko akuya, shin ya halatta mutum yaci irin naman da suke sadakarwa?
Amsa
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. A'a bau halatta mutum yaci duk wani naman da ba'a yankashi domin Allah ba.
Allah yace: "AN HARAMTA MUKU CIN MUSHE, DA JINI, DA NAMAN ALHANZIR (ALADE) DA KUMA ABINDA AKA AMBACI WANIN ALLAH DOMINSA".
(Ma'idah ayah ta uku).
Don haka bai halatta kuci wannan SADAKAR tasu ba. Tunda suna yinta ne domin neman yardar Aljanunsu da suke hulda dasu.
WALLAHU A'ALAM.