Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu mutum biyu bisa zarginsu da laifin yaudarar mutane ta hanyar bayyana kansu a matsayin aljanu suna karbar kudi daga jama’a.
Mutanen Musa Bashir da Musa Habbeeb da shekarunsu ba su wuce 35 ba, Aminiya ta samu bayanin cewa Musa Bashir ya yin amfani da muryar mata inda ya rika yi wa wani mai suna Nadabo Ibrahim dan asalin garin Gezawa waya tare da bayyana kansa a matsayin aljana da za ta taimaka masa a al’amuransa na rayuwa.
Asirin Musa ya tonu ne a lokacin da ya nemi Nadabo ya ba shi Naira dubu 80, inda a wajen karbar kudin ne jami’an Hukumar Hisba suka kama shi a Unguwar Fagge.
Nadabo ya shaida wa Aminiya cewa: “Wata rana ne aka kira ni a waya sai na ji muryar mace inda ta bayyana kanta a matsayin aljana, wacce wai na taba ba wa sadaka a wani lokaci, don haka ta yi alkawarin saka min da alheri a wannan karon.”
Malam Nadabo ya kara da cewa “Sai aka nemi na ba da wasu kudi ta hanyar tura katin waya na Naira dubu 20 da yake na gaskata cewa matar aljannar ce sai na na tura katin kamar yadda aka bukata. Abin da ya sa na gasgata hakan saboda matar ta gaya min abubuwa da dama da suka hafi rayuwata har da batun gidana da sauransu. Daga bisani sai aka bukaci na ware wani daki a gidana na ajiye farin kyalle da Alkur’ani a ciki. Kuma aka ce kada na bar kowa ya shiga dakin, washegari sai aka nemi in shiga dakin in karanta wata sura a cikin Alkur’ani sau dari.”
Nadabo ya ce, asiri ya tonu ne lokacin da aka sake neman in bayar da Naira dubu 80 za su turo wakilinsu ya karba. “To daga nan ne jikina ya yi sanyi, don haka sai na nemi shawarar wani abokina inda ya ce, mu sanar da Hukumar Hisba. Lokacin da ya zo ya karbi kudin a hannuna sai jami’an Hisba suka kama shi,” inji shi.
Musa ya ce ya koyi wannan harka ce sakamakon yadda wani ya taba yaudararsa ta irin wanann hanya har ya yi asarar gida da motarsa. “Wani mutum ya taba kira na a waya cewa daga Sakkwato yake inda ya ce zai taimake ni. Ya sa na rantse da Alkur’ani cewa ba zan gaya wa kowa abin da ake ciki ba, daga nan ya sa na rika kai masa kudi a wani kauye da ke hanyar Jami’ar North West ina ajiyewa har sau bakwai, har na rasa gida da motata,” inji shi.
Sai dai kuma, bayan jami’an Hisba sun kama mai karyar aljannun sai aka gano abokinsa da ke sintirin neman belinsa, wato Musa Habeeb tare suke gudanar da wannan mugun aiki. Musa Habeeb ya musanta zargin inda ya ce, ’yar uwar wanda ake zargin ne ta yi masa waya cewa akwai sakonsa a wurinta, da ya je ne ta ce Hukumar Hisba ta kama abokinsa, shi ya sa ya tsaya don ganin an sake shi.
Kwamnadan Hisba na yankin Fagge Ustaz Salisu Umar Rijiyar Lemo ya ce suna bincike Ya ce da zarar sun kammala bincike za su gabatar da su gaban kotu.