A arewa maso gabashin Najeriya wani dan kunar bakin wake ya tada bom a unguwar Amole da ke wajen Maiduguri, babban birnin jihar Borno, al'amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane.
Wani jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa dan kunar bakin waken ya kashe akalla mutane biyar.
Ya ce, ga alama, dan kunar bakin waken da farko ya yi kokarin shiga asibiti ne amma sai kawai "ya tayar da bam din, ya kashe mutane biyar, kuma goma suka ji ciwo".
Ya ce an kai dukkan wadanda suka ji raunin da kuma gawawwakin wadanda aka kashen asibiti.
Wani wanda ya ga yadda abin ya faru ya ce mutane ukku suke tare, sai dayansu ya tada bam.
Sauran ba su yi nasarar tada nasu ba. Jama'a sun bisu, amma babu cikakken bayani abin da ya faru da su, har ya zuwa lokacin aiko da wannan rahoton.
Wannan harin dai ya zo ne 'yan kwanaki kadan da kai irinsa a birnin na Maiduguri a lokacin da gwamnatin Najeriya ke matsa kaimi a yakin da ta ke yi da 'yan Boko Haram.
Title :
Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 5 a Maiduguri
Description : A arewa maso gabashin Najeriya wani dan kunar bakin wake ya tada bom a unguwar Amole da ke wajen Maiduguri, babban birnin jihar Borno, al...
Rating :
5