Sabuwar gwamnatin jihar jihar Bauchi, ta bayyana cewa ta karbo manyan motocin alfarma kimanin 28 daga jami'an tsohuwar gwamnatin jihar, wadanda suka tafi da motocin ba bisa ka'ida ba bayan kammala aikinsu.
Shugaban kwamitin karbo kadarorin gwamnatin jihar daga tsoffin jami'an, Ritaya Air Commodore Ahmad Tijjani Baba, ya shaida wa manema labarai cewa sun kuma karbo na'urorin janareton bayar da wutar lantarki da na'urorin sanyaya daki da dama, wadanda tsofofin jami'an suka yi awon gaba da su, a maimakon sanya su a ofisoshin gwamnati, tare kuma da soke lasisin wasu filaye da aka bayar ba bisa ka'ida ba.
Shugaban kwamitin ya ce jami'an gwamnatin da ta shuden sun yi warwason kayakin ne cikin kwanakin karshe na gwamnatin.
To sai dai kwamishina watsa labarai a tsohuwar gwamnatin, Alhaji Ahmed Salisu Barau, ya ce motocin da ake batun sun yi awon gaba da su, an sayar masu ne bisa tsarin aikin gwamnati.
Ya kara da dewa gwamnatinsu bata saba ka'ida ba wajen bai wa jami'an wadannan kadarori, amma idan sabuwar gwamnatin ta gano daidaikun jami'an gwamnatin da ta gabata da suka yi abin da ya saba ka'ida, to ba laifi ba ne ta ce su mayar da kadarorin.
Title :
Gwamnatin Bauchi ta kwato motoci 28
Description : Sabuwar gwamnatin jihar jihar Bauchi, ta bayyana cewa ta karbo manyan motocin alfarma kimanin 28 daga jami'an tsohuwar gwamnatin jihar, ...
Rating :
5