Katafaren kamfanin Intanet na Google, ya nemi gafara
daga Firayi Ministan India, Narendra Modi, bayan da
hotonsa ya bayyana a sakamakon wani bincike na manya-
manyan masu tafka laifi goma na duniya.
Kamfanin ya ce an samu wannan kuskure ne saboda
yanayin da ake bayyana hotuna a Intanet yana iya bayar
da samako bai ban al'ajabi ga wasu binciken da ake
gudanarwa.
Hoton na Narendra ya fito baro-baro tare da hotunan
Osama Bin Laden da kuma mutumin nan Dawood Ibrahim
wanda ake zargi da kai harin bam na Mumbai a shekara ta
1993.
Neman gafara ta kamfanin google ta zo ne bayan da yan
siyasa masu yawa a India da masu sharhi suka bayyana
damuwarsu a shafukan sada zumunta.
To sai dai duk da neman gafarar har yanzu hoton na Mr
Modi ya na fitowa a jerin hotunan mutane goma da suka fi
tafka manya manyan laifuka a duniya