BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Mafi dawwamar salatin Allah da amincinsa su Qara tabbata abisa Shugaban dukkan Annabawa da Manzanni, Kuma Ma'abocin matsayi abin yabo.. Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Shiryayyu.
RUKUNAN AZUMI
~~~~~~~~~~~~
Azumi yana da rukunai guda biyu. Sune NIYYAH, da kuma KAMEWA DAGA JIMA'I DA CIN ABINCI tun daga hudowar alfijir na gaske har izuwa faduwar rana.
1. NIYYAH: Kamar yadda muka sani cewa niyyah farillah ce acikin kowacce ibadah, kamar sallah, Zakkah, Hajji, to hakanan acikin Azumi ma.
Kai harma da dukkan wata ibadah wacce bayin Allah suke yinta domin neman kusanci da Allah Ubangijin Talikai.
Kamar yadda muka fada acikin babin alwala tun farko, Niyyah ita ce yin nufi azuciya adaidai farkon aikata ita ibadar da za'ayi.
Ya zamto mutum ya halarto niyyar aikata aikin adaidai lokacin da yake aikata rukunin farko da wannan aikin.
Amma sai dai shi Azumi ba'a shardanta cewa niyyarsa ta kasance tare dashi ako yaushe ba. Domin kuwa ya halatta agabatar da niyyarsa tun kafin daukar Azumin. (In dai an riga an ga wata).
Lokacin yinta shine dare gaba dayansa.
Misali: Mutum zai iya daukar niyyar azumi bayan faduwar rana. Aranar Qarshe ta watan Sha'aban (idan kwana 30 yayi kenan). Kuma niyyarsa tayi. kuma ta inganta.
★ Hakanan mutum zai iya daukar niyyarsa tun farkon lokacin da ya samu labarin ganin wata.
★ Hakanan wanda ya farka har yayi suhur, to koda bai furta niyyar da bakinsa ba, to wannan yin suhur din ya wadatar masa.
Yin wannan Suhur din ya tsaya masa amatsayin DAUKAR NIYYAH kenan ba tare da ya furta ba. Domin kuwa ita niyyah aiki ne na zuciya. Kuma yin wannan suhur din ya nuna cewa ya riga ya nufi yin azumin kenan. Dukkan Malamai sunyi ittifaki akan wannan.
MAZHABIN MALIKIYYAH sun shardanta cewa wajibi ne niyyar kowanne azumi ta rigayi hudowar alfijir. Ko azumin farillah ne ko na nafila.
Suna kafa hujjah ne da Sahihin hadisin da Imamu Ahmad da Ibnu Hibban suka ruwaito daga Nana Hafsatu Uwar Muminai (ra).
Cewa Manzon Allah (saww) yace: "DUK WANDA BAI YI NIYYAR AZUMI KAFIN HUDOWAR ALFIJIR BA, TO BABU AZUMI AGARESHI".
Wato azuminsa bai inganta ba.
MAZHABOBIN SHAFI'IYYAH DA HANBALIYYAH kuma suka ce: Ya wajabta ayi niyyar azumi kafin Alfijir acikin Azumin farillah ne kawai. Amma banda na nafilah.
Suna kafa hujjah ne da hadisin nan wanda Imamu Muslim da Ahmad suka ruwaitoshi daga Nana Aisha Uwar Muminai (rta) tana cewa:
"Manzon Allah (saww) ya kasance yakan zo wajenta yace mata "SHIN AKWAI ABINCI AWAJENKU?
Idan suka ce masa "A'A BABU" yakan ce "TO TUNDA HAKA NE, NI INA AZUMI KENAN".
Kun ga anan ya dauki niyyar Azumin kenan da safe, bayan fitowar rana. (Amma fa azumin Nafila ne ba na farillah ba).
3. MAZHABIN HANAFIYYAH su kuma sunce: Bai lazimci mutum cewa lallai sai niyyarsa ta rigayi alfijir ba, akowanne AZUMI MU'AYYANI. (wato wanda aka ayyana masa lokaci) kamar Watan Ramadhan, kamar azumin bakance wanda aka ayyana masa lokaci. Hakanan Azumin Nafila ma.
Suka ci gaba da cewa: Amma duk azumin da bashi da wani lokaci mu'ayyani, kamar Azumin Ramuko, ko Azumin Kaffara, ko Azumin bakance wanda mai yinsa bai ayyana lokaci ba, to LA BUDDA (babu makawa) sai niyyarsa ta gabaci hudowar alfijir.
Dalilin da yasa Malaman Mazhabin Hanafiyyah suka rarraba wannan hukuncin niyyah tsakanin Azumin Wajibi wanda aka ayyana masa lokaci da kuma Azumin Wajibi wanda ya ratayu da mutum,
Sunce saboda shi Azumi Mu'ayyani (kamar na ramadhan) yana da lokaci kebantacce wanda ake yinsa aciki.
To wannan kebantuwar lokacin nasa, shine ya tsaya masa amatsayin NIYYAH.
Azumin da ya ratayu da mutum kuwa, kamar Kaffara ko Ramuko, to bashi da wani lokaci kebantacce wanda ake yinsa acikinsa. Don haka suka ce wajibi ne niyyarsa ta gabaci hudowar alfijir.
Maganar Shafi'iyyah da Hanbaliyyah tana da madogara, amma ita Madogarar Malikiyyah (Musamman idan an koma Usulul Fiqhi) kuma tafi ihtiyadi.
SHIN WAJIBI NE KOWANNE DARE SAI ANYI MASA TASA NIYYAR DABAN, KO A'A?.
Malamai sunyi sabani akan haka: Sun rabu gida biyu.
★ 1. SHAFI'IYYAH, HANBALIYYAH DA HANAFIYYAH suka ce wajibi ne kowanne dare sai anyi masa niyyarsa daban. Kuma kafin alfijir.
Domin kuwa su awajensu, kowacce rana ta Ramadhan, Ibadah ce mai zaman kanta.
★ 2. MAZHABIN MALIKIYYAH : sun ce wajibi ne Qulla niyyah adaren farko na Ramadhan. Amma asauran dararen, ya zama Mustahabbi ne. (Ko mutum bai kulla ba babu komai. Wancan na farko ya isa).
Malikiyyah sunce hujjarsu ita ce AI GABA DAYANSA AZUMIN WATAN, IBADAH CE DUNKULALLIYA GUDA DAYA.
Amma sunce duk wanda wani halattancen uzuri yasashi ya yanke azuminsa, kamar Jinin haila, Ko haihuwa, ko rashin lafiya, ko tafiya, tasa yasha wasu azumin atsakani, to Babu makawa idan zai sake ci gaba da Azumin sai ya sake wata sabuwar niyyar.
Maganar Malikiyyah tafi Qarfi kuma tafi sauki.
2. RUKUNI NA BIYU shine KAMEWA DAGA DUKKAN ABINDA YAKE KARYA AZUMI.
Dalili anan shine ayar nan ta 187 acikin Suratul Baqarah, inda Allah (SWT) yake cewa:
"KUCI KUMA KUSHA HAR SAI FARIN ZAREN (ALFIJIR) YA BAYYANA AGAREKU DAGA BAQIN ZAREN NA ALFIJIR". (Wato har sai Alfijir Sadiqee ya bayyana agareku daga Alfijir kazibi) "SANNAN KU CIKA AZUMIN ZUWA DARE".
Abinda wannan ayar take nufi shine: Kamewar tana farawa ne tun daga hudowar alfijir na gaske, har zuwa shigowar wani yanki na dare (wato faduwar rana).
Ya zama Wajibi ga Mumini ya kiyaye da lokacin da alfijir din yake fitowa. Idan ya rage kamar saura minti biyar, sai mutum ya kiyaye daga dukkan Muftiraat (abubuwan da suke karya azumi) domin kewayewa (ihtiyadi).
Idan kuma rana ta fadi, har ladan ya fara kiran sallah, to ya halatta mutum yaci abinci.
Gaggauta yin buda-baki yafi alkhairi fiye da jinkirtashi kamar yadda zamuji nan gaba insha Allah.
Anan zamu dakata sai gobe kuma insha Allahu Zamuyi magana akan Sunnonin azumi da Mustahabbansa.
Salatin Allah da amincinsa madawwama su tabbata abisa babban Masoyin Allah, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa baki daya da dukkan Sahabbai.
NOTE : Wannan ma karatunmu ne tun na shekarar da ta gabata.