BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
Allah kayi salati da aminci abisa zababben zababbu, Annabinmu Manzonmu kuma Shugabanmu Muhammadu, tare da iyalan gidansa Inuwar al'ummah, da Sahabbansa Jagororin gaskiya.
Yau insha Allahu zamu Qarasa magana akan Falalar Azumi sannan muci gaba da bayani akan rabe-raben Azumin da kuma falalar watan Ramadhan.
4. Hadisi daga Sayyiduna Abu-Umamah Albahily (ra) yace:
"Nazo wajen Manzon Allah (saww) nace masa: "Ka Umurceni da wani abinda zan aikata wanda zai shigar dani Aljannah".
Sai yace min "NA HOREKA DA YIN AZUMI. DOMIN HAKIKA BASHI DA MAKAMANCI".
Sai na sake dawowa wajensa karo na biyu (Na sake tambayarsa akan haka). Sai yace min "NA HOREKA DA YIN AZUMI".
(Imamu Ahmad da Hakim da Nisa'iy ne suka ruwaitoshi).
5. Daga Sayyiduna Sahlu bn Sa'ad Assa'idy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"HAKIKA ALJANNAH TANA DA WATA QOFA WACCE AKE KIRA "RAYYAAN".
IDAN RANAR ALQIYAMA TAYI, ZA'A CE "INA MASU AZUMI!!" (SAI SUZO SU SHIGA TA WANNAN KOFAR). SAI SUN GAMA SHIGA SANNAN ARUFETA".
(Imamul Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).
FALALAR WATAN RAMADHAN
~~~~~~~~~~~~~~~~~
Hadisi daga Sayyiduna Abu-Hurairah (ra) yace:
"Yayin da Watan Ramadhan ya kama, Sai Manzon Allah (saww) yace:
"HAKIKA WATA MAI ALBARKA YAZO MUKU, ALLAH YA FARLANTA MUKU AZUMTARSA.
ACIKINSA ANA BUDEWA KOFOFIN ALJANNAH, KUMA ANA RUFEWA KOFOFIN JAHEEMU. KUMA ANA DAUREWA SHAITANU.
SANNAN ACIKINSA AKWAI WANI DARE GUDA DAYA WANDA YAFI DARARE GUDA DUBU ALKHAIRI.
DUK WANDA AKA HARAMTA MASA ALKHAIRIN (WANNAN WATAN) TO HAKIKA AN HARAMTA MASA DUKKAN ALKHAIRI".
(Ahmad da Nisa'iy da Bahaqy ne suka ruwaitoshi).
2. Hadisi na biyu daga Abu Hurairah (rta) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"SALLOLIN NAN GUDA BIYAR DA KUMA SALLAH JUMA'A ZUWA WATA JUMA'AR, DA KUMA RAMADHAN ZUWA WANI RAMADHAN DIN SUNA KANKARE ZUNUBBAN DA SUKE TSAKANINSU, IDAN AN NISANCI KABA'IRORI".
(Imamu Muslim ne ya ruwaitoshi).
3. Hadisi na uku daga Abu-Sa'eed Alkhudry (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YA AZUMCI RAMADHANA KUMA YA KULA DA DOKOKINSA, KUMA YA KIYAYE DAGA DUK ABINDA YA KAMATA YA KIYAYE, TO ZA'A KANKARE MASA DUKKAN ZUNUBANSA DA SUKA GABATA"
(Imamu Ahmad da Nisa'iy ne suka ruwaitoshi da Isnadi mai kyau).
4. Hadisi na hudu daga Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YA AZUMCI RAMADHAN YANA MAI IMANI DA KUMA NEMAN LADA, AN GAFARTA MASA ZUNUBANSA DA SUKA GABATA".
(Imamu Ahmad da Nisa'iy da Baihaqy da Abu Dawud da Tirmizy ne suka ruwaitoshi).
Hakika idan mutum yayi nazari acikin ma'anoni da dambin falalaar da wadannan hadisai suka Qunso dangane da Watan Ramadhan da kuma Ibadar Azumin da akeyi acikinsa, to babu abinda zamu ce ma Allah sai dai godiya agareshi da ya bamu Wannan Annabi mai girma, wanda albarkacinsa ne aka bamu wannan watan na Ramadhan.
Anan zamu tsaya sai gobe insha Allahu zamu ci gaba. Da fatan Allah shi karba mana dukkan ibadunmu. Kuma Allah ya sanyamu cikin bayinsa wadanda yake 'Yantawa awannan watan. Albarkacin hasken Alqur'anin da aka saukar acikinsa..
NOTE : Wannan maimaicin karatunmu ne na Azumin Bara.