Dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook ya bude ofishinsa na farko a Afrika.
Kamfanin shafin ya bude ofishin ne a, Johannesburg, babban birnin Afrika ta Kudu.
Kamfanin ya ce yana da mutane miliyan dari da ashirin, masu amfani da shafin a Afrika.
Kaso 80 cikin 100 kuma cikinsu, suna shiga shafin ne ta wayar salula.
Kamfanin ya kara da cewa zai fara ne da bunkasa kasuwanci a kasar Kenya da Najeriya da kuma Afrika ta kudu.