¤
1 → Kowanne mutum burinsa shine ya auri matar kirki, wacce zata zama uwar yayansa, to tambaya anan shine wa kake tunanin zai auri wacce ka lalata?
+
+
+
2 →
Babu wanda zai so yaga kanwarsa ko yarsa ta lalace, kai me yasa kake kokarin lalata yar wani?
To kaga rashin adalci kiri-kiri kenan.
+
3 →
Kowanne dan adam baya son a yaudareshi ko aci amanarsa, dan me kake kokarin yaudarar wani ko cin amanar wani?
Kamar fa yadda kake jin radadi idan an yaudareka to haka fa kowa yake ji, kaga ashe abin ba dadi. Hakika dole sai mun yiwa kanmu adalci kafin wani yayi mana,
sai zukatanmu sun gyaru kafin al'umma ta gyaru, kamar dai yadda idan zuciya ta gyaru to dukkan jiki ya gyaru.
:
Tabbas idan irin wadannan tunanin suna shawagi a nahiyar kwakwalwarmu babu yadda za'ayi a sami gurbatacciyar al'umma.
:
YA ALLAH KA RABAMU DA SON ZUCIYA,
KA SHIRYAR DAMU, KA TSARKAKE ZUCIYARMU DAGA WASIWASIN SHAIDAN LA'ANANNE.......