Hamshakin Attajirin Afrika Aliko Dangote ya ce yana kan bukatarsa ta mallakar Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a Ingila Dangote ya shaidawa wakilin RFI Hausa Abubakar Isa Dandago cewa shi masoyin Arsenal ne tsawon shekaru 30.
Dangote ya fadi haka ne a lokacin da ke kaddamar da shirin zuba jarin kudi Dala miliyan 250 a Jihar Jigawa wajen noman Shinkafa da Suga a Jihar.
Tun a watan Mayu ne rahotanni ke cewa Dangote yana da kudirin sayen Kungiyar Arsenal.
Na dade ina sha’awar Arsenal, inji Dangote.
Kuma ya ce idan dai batu na kudi ne yana da tabbacin zai iya saye Arsenal.
Title :
Dangote ya dade yana sha’awar Arsenal
Description : Hamshakin Attajirin Afrika Aliko Dangote ya ce yana kan bukatarsa ta mallakar Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a Ingila Dangote ya shaidawa ...
Rating :
5