Safiya tanayi wadanda akayiwa sata suka iso
station suka samemu aka fito dani aka tambayeni
ina kaya? Nace nifa ba barawo bane yan sandan
suka mai dani akasa wasu mutum biyu su
tambaye nan sukai ta jibgata ina ihu danaga ba
sarki sai Allah na amsa cewar ni nayi satar' nan
suka turani wajen Alkali ya yanke min wata daya'
Ina shiga prison dinnan nafara facing din wahala
kala-kala tun bana cin abincin da ake bani harma
dai na dawi dani ake kokawar karbar gabza
yazamana na fara sabawa da wannan rayuwar
aciki na hadu da wani guy auwal Allah ya hada
jininmu sosai komai tare mukeyi watarana muna
zaune nace auwal wai me yakawo ka prison ne?
Auwal yace kb wallahi tsautsayine yakawo ni' ya
cigaba da cewa nidan garinnan ne amma na
kasance in zuwa jos ina kai fata wani company
nayin takalma da jakunkuna watarana na nadawo
kano domin ganin iyayena natarar ana fada suka
mokota nan nashiga wannan rigimar har na jiwa
wani daga ciki ciwo kaji silar shigata prison' nace
lallai auwal na tausAya maka' auwal yace kb kai
kuma fa mene ya kawo ka prison? Nace ai ni
sharrin sata akayimin' auwal yace Allah sarki
kasanni saura kwana biyar na fita kaifa? Nace ai
nima saura kwana takwas nafita' yace abokina
yanzu idan muka fita ai zamu zama friend ko?
Nace ai insha Allah'
Kullum ba abinda muke sai aiki acikin wajennan
ranar juma'a da safe gandurova suka shigo aka
kira wadanda za'a sallama harda auwal nan
mukai bankwana yace min ranar litinin zaizo idan
anfitar dani akan haka muka rabu da auwal'
Haka naci gaba da zama ni kadai batare da
auwal ba kullum sai tunanin dangina nake dama
auwal ne yake debemin kewa gashi kuma shima
yatafi ba abinda nake tunawa sai photon salmah
dayake cikin jakar nan da take hannun police'
azuciyata nace ni yanzu idan ma nafita ina zan
dosa ni gashi ba wanda nasani sai ummah da
daddy sai salmah haka dai nayita sake-sake
azuciyata amma ban samu mafita ba' gari yana
wayewa aka zo dan fitar damu ina fitowa waje
naga auwal shida wata yarinya' aguje awal
yakaraso inda nake yace abokina barkanka da
fitowa nace Hmm auwal ai nazata kamanta dani'
auwal yayi dariya yace haba tayaz an manta da
kai yace wannan itace kanwata yasmin na kalleta
naga ta hade rai' nace malama yasmin! Ta juyo
tace oh! Sannufa' naga sam kamar bataji dadin
ganina ba' auwal yace abokina mukarasa gidanku
ko? Wani gumi ya karyo min nace auwal zo kaji'
yadan dawo gefe mukabar yasmin anan' nace
abokina na manta ban fadamaka wani abuba'
auwal yace menene? Nace gaskiya ni maraya ne
kuma ba a garinann nake ba nazo wajen kanin
babana ne domin nadanyi sana'a sai natarar ya
rasu yanzu hakama kayana suna wajen police'
auwal yace Allah sarki abokina ai ban saniba
yanzu muje wajen police ka karbi kayan sai mu
karasa gida' nace to abokina
Tunda mukaje gidansu auwal na tarar suma su
ukune dagashi sai kanwarsa yasmin sai kuma
ummansu shima mahaifisu yarasu' ummansu
tana nuna min kauna kamar dan data haipa
amma sam yasmin batason ganina agidansu
bansan me nayi mata ba' tuni auwal yasamomin
machine adai-daita sahu na fara ja ina neman
kudi' shikuma yashirya dan komawa jos dan
cigaba da aikin fatarsa' naso in bishi amma
auwal yacemin nabari idan yaje komai ya dai-
daita zai kirani haka mukai sallama dashi
yabarmin amanar danginsa'
Nanfa naci gaba da jan machine dina kullum
nadawo mu zauna da umma muyita hira amma
yasmin sam ban taba burgeta ba' watarana na
hau titi ina ta tuki wasu mata suka tsaidani suka
shiga' muna cikin tafiya wata daga cikinsu tace
lah! Wai wannan ba dan Alhaji bane yayan
salmah da mukaje birthday dinsa? Nan naji
gabana ya fadi nace a'a bashi bane ni inaji dai
munyi kama ne' wata daga ciki tace gaskiya
amma kamar ta baci' wata daga ciki tace Allah
sarki salmah ko ina tayi' wata tace kai gaskiya
wannan yayan nata bashi da mutunci wai ace yar
uwarka ka koreta bakasan inda zataba' wata tace
Kiduba dai yanda salmah take sonsa amma yayi
mata haka' suna fadin haka nikuma hawayene
kawai yake zuba daga idanu na' suka sauka
Awwal ya kirani yace kb mun gama magana da
manager company dan haka kashirya gobe ma ka
taho kawai nace yauwa abokina' na fadawa
ummah' washe gari da sassafe na dau hanya
daga kano na nufi jos' ina zuwa na kira wayar
awwal yazo ya daukeni' muka karasa naci abinci
nayi wanka' awwal yadan fita nikuma na bude
jakata na dakko photon salmah nasa agaba ina
kallo' ina tunanin yanda rayuwa ta juyamin wai
yau nine a wani gari dan neman aikinyi' na maida
photon na tashi na tafi masallaci nayi sallar isha
na roki Allah ya yafemin laifin danayi masa'
Washe gari muna zaune da awwal yacemin kaga
wannan mai company badai dukiya ba' nace Allah
yace kuma kasan wani abun mamaki? Nace a'a
yace macece fa da companin' nace Allah
abokina? Yace wallahi gashi kaga duk wannan
kudin nata amma sam taki tayi aure' nace
meyasa? Yace wallahi ba wanda yasani amma
gaskiya tana da kirki dan karkaso kaga yanda
take jan mutane ajiki tana taimaka musu' shiyasa
ma na kawoka tunda kai kayi nisa akaratu idan
Allah yataimakeka tayi maka inter view kaci sai
kaga an daukeka aiki' nace to abokina Allah
yasa' yace ameen
Ranar laraba muka tafi office din manager da
takarduna muna zuwa muka tarar ancika' awwal
yace to kb sai fa kabi layi' nace abokina ai ba
komai haka na dasa layi ina jira azo kaina' saida
layi yakusa zuwa kaina akace angama lokaci yayi
sai dai gobe' haka na juyo cikin bakin ciki
nadawo'
Bayan awwal yadawone ya tambayeni abinda
yafaru nafada masa yace kayi hakuri gove sai
kaje da wuri' nace yauwa auwal dama inaso na
tambayeka' yace ok kb inaji' nace wannan
kamfanin guda dayane amma naga anata dibar
ma'aikata dayawa' Auwal yace Hmm kb kenan ai
ba kamfani daya bane kamfaninta acikin garinnan
sun ka hudu kuma duk sunansu daya' nace mene
sunansu? Yace ai duk wani waje indai natane
zakaga sunan sa' (SK) nace lallai tanada dukiya
Misalin karfe takwas muka tafi wajen inter view'
muna cikin tafiya wata yarinya ta shararo mota
da gudu ta kusa bugemu kuma ta fito tana mana
masifa' nayi shiru ina kallonta shikuma auwal
yadinga fada mata magana' nace awwal muje
rabuda ita' muka wuce' awwal yace kai abokina
Allah ya kawo randa muma zamuse mota kamar
waccen ace tamuce' nayi murmushi nace ameen
Awwal amma kasan wani abu? Yace a'a' nace a
shekara biu da suka wuce na bada kyautar
motocin da sukafi waccen tsada' Awwal ya juyo
da sauri yace kb da gske kake? Nace kwarai
kuwa amma dogin labarine kabari sai mun samu
time' awwal yace to abokina
Muna karasawa nahau layi awwal yatsaya agefe
da yake yau bashi da aiki' mutum biyune suka
shiga saini' na danna kai office' abinda nagani
yayi matukar firgitani na tsaya cak! Bakowa bace
face salmah a zaune take akan kujera' tasa suit
baka tayi kyau matuka kanta a sunkuye yake tana
rubutu' tace shigo mana batare da ta dago kanta
ba' nikuwa ina tsaye na kasa gaba na kasa baya'
salmah ta dago mukai ido hudu da ita' tamike
afirgice tace yaya kabeer!! Wani hawaye ya
gangaro daga idanuna' na juya na fito da sauri
salmah ta biyoni tana cewa yaya kabeer! Jama'ar
da suke wajen suka tsaya suna kallon ikon Allah'
awwal yatsaya yana mamaki' salmah tasha
gabana' na tsaya na sunkuyar da kaina kasa'
tace haba yaya meyasa zaka juya kafita bayan
na dade ina nemanka yau fa banfi sati daya da
dawowa daga kano ba akace min ba'a san inda
kake ba kullum ina cikin damuwa yaya' na kalleta
nace kanwata ban cancanta ki yafemin ba'
shiyasa ma ban nemi hakanba' salmah tace haba
yayana dan Allah muje gida tukunna' na kira
awwal ya karaso inda muke shidai mamaki duk
ya baibayeshi' nace awwal wannan kanwatace'
auwal yatsaya yana mamaki' nan muka shiga
mota sai wani tamfatsetan gida muna zuwa aka
kawo mana abinci kala-kala
Na kwashe labarina kaf nafa dawa salmah awwal
yanaji Allah sarki ina fadamata tana kuka saboda
tausayina' danazo karshe a labarinne tace sannu
yayana gsky na tausaya maka' itama ta fara bani
nata labarin tace tunda nabar gida banzame ko
ina ba sai nan jos gidansu wata qawata nake
zaune ahankali nafara juya dukiyata har Allah ya
kawo ni wannan matsayi yanzu haka ina da
companies a garuruwa uku bayan jos kuma duk
anayin takalma ne da kuma jakunkuna na mata'
wannan gidan da kk gani aciki nake saukar
abokan kasuwancina' yaya yanzu tunda Allah ya
kawo ka komai nawa zai dawo karkashi
kulawarka' saboda mijina yadawo dama shi nake
jira' cikin sauri nace dama kinyi aure ??? Tayi
dariya tace zandaiyi yaya' nace waye kuma
mijin?? Tazaro wayarta tace ga pic dinshi a
screen din wayata' na karba jikina a sanyaye dan
ganin wanene wannan ya canzawa salmah ra'ayi'
ina dubawa naga photona wani dadi ya kamani
nace salmah dama har yanzu kinasona? Tace
yaya ai bazan iya mantawa dakaiba tun ina
karama nakesonka har na girma'
Watanmu biyar da haduwa da salmah iyayen
kawarta sukayi mana aure nazama nine manager
awwal kuma yazama shine mai kula da wani
kamfanin' muna zaune nida salmah na kalle ta
nace wai kanwata in tambayeki mana? Tace
yayana ina jinka' nace wai menene meaning din
wannan sunan kamfanin nan (SK)?? Salmah tayi
murmushi tace (SALMAH KABEER) na kalli
salmah wani hawaye ya zubo daga idanuna'
salmah tace lafiya yaya? nace salmah dan Allah
ki yafemin' tace haba yaya dan Allah kamanta da
wannan zancen
Mukaita shan soyayyarmu nida salmah watarana
zan zo kano akan wani business salmah tace
zata biyoni muka taho tare bayan mun gama
harkar ne na cewa salmah mu karasa
unguwarmu' muna shiga layin naga unguwar duk
ta canza muka karasa wajen wani taron jama'a
muna zuwa muka tarar da su hamza ne suke
fada akan kudi harda rukhy sai kallonsu ake
muka karasa nayi musu sallama gaba dayansu
suka juyo suna kallon mu ' dukkansu suka kama
mamaki nace nawane kudin' kowa yayi shiru
nadanyi murmushi nace Hmm hamza kenan ai
duk wanda yayi rubutu ba dai-dai ba dole ya
goge yasake' ni nayi na nagyara ku kuma yanzu
zaku gyara naku' ke kuma rukhy ga mata ta na
nuna musu salmah kowa ya sunkuyar da kai'
nace musu nabarku lafiya muka juya muka shiga
mota' jama'a suna kallonmu""""""THE END