Hadisi yazo acikin Dala'ilun Nubuwwa na Baihaqiy, cewa akwai wasu Mata guda biyu wadanda sukayi azumi azamanin Manzon Allah (saww).
Amma maimakon su shagaltu da ibada, sai suka zauna su a gulmar Mutane. saboda haka da lokacin shan ruwa (buda baki) ya Kusa, sai wannan naman mutanen da suka ci yazo ya shaje musu wuya. suna yin numfashi da kyar!!
Aka zo aka gaya ma Manzon Allah (saww) cewa ga wasu nata nan zasu mutu. Basu iya yin magana, ko numfashi ma da kyar suke yi.
Manzon Allah (saww) yayi umurni aka kawosu Gabansa. Sai yasa aka kawo wani Qoko (kwarya) aka ajiye agabansu. Nan take suka fara yin AMAI, suna ta amayar da Rubabben naman mutane da kuma 'diwa (wani ruwa mai wari kamar ruwan gyambo).
Shine Manzon Allah (saww) yake bada labari akansu, yace "Sun zauna ne suna gulma (wato cin naman mutane). shi yasa wannan abun ya faru akansu.
'Yan uwa sai mu kiyaye harshenmu, mu san irin maganganun da zamu rika furtawa. Idan ba haka ba, zamuyi asarar ladan azuminmu (Allah shi kiyayemu).
DAGA ZAUREN FIQHU.
Title :
CIN NAMAN MUTANE DA AZUMI
Description : Hadisi yazo acikin Dala'ilun Nubuwwa na Baihaqiy, cewa akwai wasu Mata guda biyu wadanda sukayi azumi azamanin Manzon Allah (saww). Amm...
Rating :
5