Misalin 12:20Am. Nagama kintsawa Nayi shirin
kwanciya daga ni sai Tiri kwata Wanda nasaba
sawa Idan zan kwanta.
Bayan na kwanta sai na fara tunani a cikin
Zucuya ta
Naje Gidan su budurwa ta ASMA'U Daga nanuna
mata kosawa ta akan In turo gidan su ayi
maganar Aurenmu shine tafara man Fada Har
nafahimci bata sona kudi kawai take so Ina tunin
nahakura da ita koko? Amsar danaka samu,
Ihun da
naji ne ya dawo dani daga gajeren
tunanin danake akan Asma'u Tabbas
na gaskata abinda kunnuwa na suka
jiyo min, Ihun mace ne daga can waje.
Nayi maza na sanya doguwar riga na
dauki torch light mai hasken tsiya
kamar fitilar masu gadi na fita.
Mutum biyu na hanga acan gaba kadan
cikin Daren suna kokarin kama
wata matashiyar budurwa tana zizzille
musu. Hasken fitilata ne ya sanya
mutanen suka juya a guje suka kule a
cikin
duhu. Nayi maza na karasa wurin da
yarinyar ke tsaye tana karkarwa kamar
wacce ake ma gangi.
''Zo mu gudu'' nace cikin yanayin tsoro.
Gyada kai tayi alamar a'a ba zata tafi
ba, tun kafin ta ankara na fisgi
hannunta cikin nace mu bar nan wurin
tun kafin su dawo su same mu don
abinda yasa suke gudu sun zata bani
kadai bane. Na kashe fitilar dake
hannuna duhu ya mamaye wurin muka
ruga a guje ni da ita, muna zuwa kofar
gida na nayi maza na
bude muka shiga na mayar da kofar na
rufe. Na shige gaba ta bi ni a baya, duk
da na lura har yanzu
tana cikin matsananciyar kaguwa da
tsorata.
Kai tsaye na shige cikin falo na kunna
wutar lantarki haske ya wadata a dakin,
inda anan ne na lura da
raunin da suka ji mata a kafarta da
hannunta. Nayi maza na dauko akwatin
first aid nayi dressing din
ciwon sannan na mike nace mata ki
saki jikin ki, ban kawo ki nan don cutar
dake ba sai don taimakon ki. Nan da
kike gani gida na ne kuma ni kadai ne a
ciki ba kowa, don bani da mata. Ban
bari tayi magana ba
nace mata ina zuwa! Na juya da sauri
na shige daki na nashiga tunanin wani
irin kaya zan bata ta sauya
don gabadayan kayan dake jikinta a
yage suke Don mutanen Da suka tare ta Suke
kokarin mata fyade Sun yaga mata riga
Na dauko mata wata rigata ta 'yan kwallo Nabata
nace tasa Na dakko wando Na na Kot dina
nabata nace tasa
Ta Amsa cikin tsoro Alamun Haryan zu na jin
tsoro na
Bayan tasa
naje cikin Firij na dakko mata Lemu da wani
guntun bred Na mika mata ta Ansa
Nace mata Idan kingama ki kwanta a Dakin dake
Bayan ta sai Ta amsa da to,
Naje na kwanta Ina jiran gobe tayi na Tambayeta
Me takeyi acikin Daren jiya,.....by I.m.s & s.khalifa........to be continue........