Dan kwallon Argentina Carlos Tevez ya kammala komawa Boca Juniors daga kulob din Juventus na Italiya.
Tevez mai shekaru 31, ya fara taka leda a matsayin kwararren dan wasa a Boca, yayin da ya bar kungiyar ya koma buga tamaula a shekarar 2004 a nahiyar Turai.
Tsohon dan wasan Manchester United da Manchester City da kuma West Ham ya zura kwallaye 20 a gasar Serie A da aka kammala a Juventus.
Tun a baya an yi ta hasashen cewar Tevez zai koma taka leda a Liverpool ko Atletico Madrid ko kuma Paris St-Germain.
Tuni Juventus ta maye gurbin Tavez, a inda ta dauko Mario Mandzukic daga Atletico ta Spaniya.
Title :
Carlos Tevez ya koma Boca Juniors
Description : Dan kwallon Argentina Carlos Tevez ya kammala komawa Boca Juniors daga kulob din Juventus na Italiya. Tevez mai shekaru 31, ya fara taka le...
Rating :
5