Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnonin jihohin kasar cewa zamanin yi wa doka karan-tsaye da almundahana da dukiyar al'umma ya wuce.
Buhari, a tattaunawarsa da gwamnoni a fadarsa ta Aso Rock, ya sha alwashin kwato duk kudaden da tsofaffin jami'an gwamnati suka sace.
"Watanni uku masu zuwa za su kasance masu tsauri, amma kuma za mu yi iyaka kokarinmu domin kwato biliyoyin dalolin da aka sace," in ji Buhari.
Shugaban kasar ya yi alkawarin mayarwa gwamnonin jihohi kudaden da suka kashe wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a kan gwamnatin tarayya.
Buhari ya kuma jaddada cewar daga yanzu ba za a dinga saka kudaden harajin da gwamnatin tarayya ta ke samu ne a asusun gwamnati sabanin yadda a kan yi a gwamnatocin baya da ake ware wasu kudade da danyen mai a zuba a wani asusu daban.
A nasu bangaren, gwamnonin sun bukaci shugaban kasar ya duba matsalolin da suka janyo tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya sa wasu jihohi suka gaza biyan albashi na watanni da dama.
Title :
Buhari ya gargadi gwamnoni Akan Cuwa-Cuwa
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnonin jihohin kasar cewa zamanin yi wa doka karan-tsaye da almundahana da dukiyar al'umma ya wuc...
Rating :
5