Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari bai shiga fadar shugaban kasa ba watau Aso Rock a ranar farko da ya fara aiki a matsayin shugaba.
A duk tsawon ranar Litinin, Shugaba Buhari ya yi aiki ne daga gidan da shugaba mai-jiran-gado kan zauna kafin a rantsar da shi wanda aka fi sani da Defence House.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta shaida wa BBC cewa shugaban ya ci gaba da kasancewa a gidan ne (Defence House) saboda aikin gyare-gyare da har yanzu ke gudana a fadar.
Wani wakilinmu daya leka fadar ta Aso Rock ya ce ya lura da ana yi mata wasu kananan gyare-gyare kamar na sauya fitillu.
Tun bayan da aka ayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Maris ya ke zaune a Defence House.
Title :
Buhari bai koma Aso Rock ba
Description : Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari bai shiga fadar shugaban kasa ba watau Aso Rock a ranar farko da ya fara aiki a matsayin shugaba. ...
Rating :
5