Rundunar sojin Chadi ta ce ta kai hare-haren sama kan sansanonin Boko Haram da ke Najeriya, domin daukar fansar hare-haren kunar bakin wake da ake zargin 'yan kungiyar ne suka kai Njamena, babban birnin kasar.
A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce an lalata sansanonin kungiyar Boko Haram guda shida yayin hare-haren saman, wanda ya jawo asarar rayuka da dama tare da lalata kayayyyaki.
Sanarwar, ta kuma ce Chadi za ta ci gaba da kai hare-hare kan 'yan kungiyar ba tare da tausayi ba, saboda daukar fansar jinin duk wani dan kasarta da suka kashe.
Hare-haren da aka kai a ranar Litinin kan hedikwatar 'yan sanda da kuma makarantar 'yan sanda a Njamena babban birnin kasar, sune na farko da aka taba kai wa babban birnin wata kasa da ba Afrika ta yamma ba, wacce take taka rawa a yakin da rundunar hadin gwiwar kasashen yankin tafkin Chadi ke yi da kungiyar.
Title :
Chadi ta yi wa Boko Haram luguden wuta
Description : Rundunar sojin Chadi ta ce ta kai hare-haren sama kan sansanonin Boko Haram da ke Najeriya, domin daukar fansar hare-haren kunar bakin wake ...
Rating :
5