Assalamu Alaikum. Allah ya qarawa malam lafiya ameen.
Malam, Allah yana cewa a cikin Alqu'ani mai girma "Nisaokum harthun lakum, fatoo harthakum anna shitum {Your wives are plantation for you, so approach your plantation or your lands as you wish"}
Tunda hakane, toh malam meye hukuncin Oral sex? Saduwar da ake yi ta baki? Malam ya halatta? Malam kuma dan Allah meye hukuncin phone sex? Wanda zaka ga wata kila idan miji da mata suna nesa da juna, sai su kira waya suna hira especially{ sexy chat} har su biya sha'awar su. Malam wannan ya halatta tsakanin ma'aurata?
{Daga Abubakar Imam Gwandu}
AMSA
--------
Eh haka ne. Allah ya fada haka. Amma ba wai ayar tana nufi cewar kuyi jima'I dasu ta kowacce Qofa bane.
A'a ayar tana nufin "KUYI JIMA'I DASU AKWANCE, KO AZAUNE, KO ATSAYE, KO DURKUSHE, KO TA-GABA, KO TA-BAYA".
Wannan shi ake nufin "annaa shi'itum" din.
Dangane da KOFAR SADUWAR kuwa, idan ka koma ayar da take kafin wannan wacce ka kawo, ai zakaga wajen da Allah yake cewa:
"FA'ATU HUNNA MIN HAITHU AMARA-KUMULLAH".
Wato: "Kuzo musu (ku sadu dasu) ta wajen da Allah ya umurceku".
To idan kayi nazari, ai zaka ga cewar FARJINSU shine wajen da Allah ya umurcemu din. Ba wai dubura ba, ba kuma baki ba.
Da akace MATAYENKU GONAKINKU NE, ai farjinsu shine gonar. Maniyyin mazajensu kuma shine irin da ake shukawar (seeds) kenan.
Don haka idan kazo da seeds dinka, awanne waje ya kamata ka shuka?
ABAKI??- a'a shi baki anyishi ne domin zikiri da karatun Alqur'ani da salatin Annabi (saww) dakuma cin abinci, da furuci.
Don haka bai kamata wajen ambaton Allah kuma ya koma ya zama wajen yin Jima'I ba.
Acikin littafin FATAWAL HINDIYYAH juzu'I na 5 shafi na 372, marubucin yana cewa:
Malamai sun kasu gida 2 akan mas'alar ta kowacce fuska.
Idan sumbartar al'aurar juna kawai kake nufi, ba tare da fitar Maziyyi ko Maniyyi ba, to wasu Malaman sunce ya halatta. Amma mafiya yawan Malamai sunce MAKRUHI NE.
(Aduba Tafsirin Qurtubee juzu'I na 12 shafi na 231 da kuma AL-INSAF juzu'I na 8 shafi na 33)
Amma idan kana nufin saduwa sosai harda fitar maniyyi da maziyyi, to wannan Mafiya yawan Malamai sun tafi akan rashin halaccin yinsa. Saboda wadancan dalilai wadanda na lissafa.
An tambayi Shaykh Nasiruddeen albany akan wannan Mas'alar. Sai yace:
"Haramun ne domin Wannan wani aiki ne wanda koda acikin dabbobi ma, in banda KARNUKA babu masu yi. Kuma sanin kowa ne cewar koda acikin sallah an hana muyi irin durkusowar rakumi, ko kuma irin Koton kurciya dinnan alokacin Sujadah, kuma Manzon Allah (saww) ya umurcemu mu guji yin koyi da Kafirai da mushrikai acikin al'amuran addininmu da rayuwarmu. To kaga kenan bai halatta muyi koyi dasu ayanayin saduwarmu da iyalanmu ba.
Aduba FATAWAL MUHIMMAH shafi na 709.
Kuma likitoci sun tabbatar da cewar ana kamuwa da cutar MOUTH CANCER ta wannan dalilin.
Da fatan mai tambayar ya gamsu.
Wallahu a'alam.
DAGA ZAUREN FIQHU, wannan ita ce fatawa ta 828 acikin littafinmu mai kunshe da fatawoyi DUBU da amsoshinsu. In sha Allahu yana nan tafe.