Akalla mutane 20 ne aka ba da rahoton sun rasu sakamakon harin kunar bakin wake a tashar Baga da ke Maiduguri a jihar Borno.
Mutane da dama kuma sun jikkata a harin da ake zargin mace 'yar kunar bakin wake ce ta kai.
Bayanai sun ce wata 'yar kunar wake ita ma ta tayar da bam a kusa da wani Masallaci, bayan da bam din ya ki tashi da farko.
Ana zargin kungiyar Boko Haram da kaddamar da irin wadannan hare-haren a arewa maso gabashin Nigeria, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 15,000.
Sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sha alwashin kawar da Boko Haram inda ta mayar da cibiyar bayanai kan yaki da kungiyar zuwa Maiduguri daga birnin Abuja.
Title :
Bam ya hallaka mutane 20 a Maiduguri
Description : Akalla mutane 20 ne aka ba da rahoton sun rasu sakamakon harin kunar bakin wake a tashar Baga da ke Maiduguri a jihar Borno. Mutane da dama...
Rating :
5