Mutane akalla 23 aka bayyana sun hallaka a garin Monguno da ke jihar Borno, arewa maso gabashin kasar.
Lamarin ya faru ne bayan fashewar wasu abubuwa da aka samu a wani sansannin mayakan Boko Haram da ke Marte a yammacin Talata.
Dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Monguno, Tahir Monguno ya bayyana cewar mutane 32 ne suka jikkata sakamakon fashewar bam din
'Yan bangar da ke aiki tare da sojojin Nigeria na gudanar da wani bincike ne a sansanin, lokacin da wasu daga cikin bama-baman suka fashe.
Hakan na nuni da hadarin da ke tattare da yankunan, duk da cewa an fatattaki mayakan Boko Haram din, zai kuma sa yunkurin hukumomin na barin mutane su koma gidajensu cikin sarkakiya.
Bayanai sun ce an kai gawarwakin wasu daga cikin wadanda aka kashe zuwa asibitin gwamnati na birnin Maiduguri.
Title :
Bam ya hallaka mutane 23 a Monguno
Description : Mutane akalla 23 aka bayyana sun hallaka a garin Monguno da ke jihar Borno, arewa maso gabashin kasar. Lamarin ya faru ne bayan fashewar wa...
Rating :
5