Assalamu'alaikum malam ya azumi ya iyalai ya hakuri da jama'a kuma, to Allah kasa muna daga cikin yan' tattun bayinka Ameen tambayace gareni malam wanda na ka sa sukuni. Gashi kamar haka .............watace tabani wayarta nasaida mata to an saidata #6000 sai na fada mata sai tace ta sayar Abata kudin bayan na dawone sai na hadu da kanin mai saida wayar shima shagonsu daya tare suke xama muna mutunci dashi sosai sai shikuma yace ya siya #7500 sai na siyar mai yabani kudin nikuma sai nabata #6000 narike sauran canjin shin menene hukuncin canjin danarike? Allah ya kara dau kaka, Allah ya bada ikon Amsa tamyar.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
A'a bai halatta gareka ka rike wannan chanjin ba. Ita wannan baiwar Allah din ta amince dakai ne. Shi yasa har ta baka wayarta kaje ka sayar. Kuma watakil tana cikin bukatuwa ne sosai shi yasa da farko tace ta sallama a Naira dubu shidan.
Wannan rikewar da kayi ya zama ha'inci. Kuma Allah yace "ALLAH BA YA SON MASU YIN HA'INCI".
Manzon Allah (saww) yace: "KA ISAR DA AMANA GA WANDA YA AMINCE MAKA. AMMA KAR KA HA'INCI WANDA YA HA'INCEKA".
Kuma ya lissafa cin amana daga cikin halayen Munafurci. Don haka ya kamata ka tuba zuwa ga Allah bisa wannan laifin da ka aikata. Kuma yana daga cikin Sharudan tubanka, KAJE KA MAYAR MATA DA CIKON KUDINTA, KA NEMI AFUWARTA.
WALLAHU A'ALAM.