Kulob din Arsenal na daf da daukar dan kwallon Chelsea mai tsaron raga Petr Cech.
Tuni tattaunawa ta yi nisa tsakanin kungiyoyin biyu, domin ganin dan wasan mai shekaru 33 ya koma tsaron ragar Arsenal a kakar wasannin badi.
Cech dan kwallon tawagar jamhuriyar Czech, wanda ya yi shekaru 11 a Stamford Bridge ya buga wasanni 16 da Chelsea a kakar wasan bana.
Golan ya koma murza leda Stamford Bridge ne daga kulob din Rennes na Faransa a shekarar 2004.
Arsenal wacce ta dauki kofin FA, tana yin amfani da mai tsaraon raga ne tsakanin Wojciech Szczesny ko kuma David Ospina a wasannin da take yi.
Cech ya yi wa Chelsea wasanni sama da 300, yayin da ya dauki kofunan Premier hudu da na FA hudu da League Cup daya da kofin Zakaraun Turai da kuma na Europa.
Title :
Arsenal na daf da daukar Petr Cech
Description : Kulob din Arsenal na daf da daukar dan kwallon Chelsea mai tsaron raga Petr Cech. Tuni tattaunawa ta yi nisa tsakanin kungiyoyin biyu, domi...
Rating :
5