A ranar Alhamis ne wata babbar kotun addinin musulunci da ke zama a birnin Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa mutane tara hukuncin kisa bayan samun su da laifin batanci ga annabi Muhammadu[SAW].
Kakakin babbar kotun jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya tabbatarwa da BBC hukuncin kisan, inda kuma ya ce an saki wasu mutane hudu sakamakon rashin samun su da laifi.
A kwanakin baya ne dai mutanen suka yi kalaman batancin ga fiyayyen halitta a wajen wani maulidi na Shehu Ibrahim Inyas, a birnin na Kano.
Masu furucin batancin dai suna alakanta kansu da kasancewar mambobin darikar Tijjaniyya.
Sai dai kuma wasu daga shugabannin darikar tijjaniyyar sun nesanta kansu daga kalaman.
Wata mace wadda ta shirya mauludin na daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin kisan.
Wannan al'amari dai ya jawo tashe-tashen hankula a inda mazauna birnin suka yi ta yin kiraye-kiraye da a hukunta masu batancin.
To amma yanzu mazauna birnin na Kano suna bayyana farin cikin su dangane da wannan hukunci a inda suke cewa hakan zai zama izna ga duk wanda ya ke tunanin kwatanta hakan.