Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci rundunar sojin kasar da ta cire shingayen da aka kafa a manyan hanyoyin kasar domin duba ababen hawa.
Wata sanarwa daga mai taimakawa shugaban kan yada labarai Garba Shehu ta ce za a janye shingayen ne a wuraren da zaman lafiya ya dawo, domin sojojin su fi mayar da hankali wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Shugaba Buhari -- wanda ya bayar da umarnin lokacin wani taro da manyan hafsoshin tsaron kasar -- ya ce ba za a cire shingayen ba a wuraren da sojojin suka ga ya kamata a ci gaba da amfani da shingayen.
A baya dai, 'yan kasar da yawa suna kokawa da shingayen saboda abin da suka kira takura da tsaikon da suke haddasawa ga matafiya.
Gwamnatin kasar ta kakkafa shingayen ne a baya da nufin yaki da barazanar masu tayar da kayar baya.
Title :
An umurci soji su cire shingaye a Nigeria
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci rundunar sojin kasar da ta cire shingayen da aka kafa a manyan hanyoyin kasar domin duba ababen...
Rating :
5