Mazauna Maiduguri na jihar Borno da ke arewacin Najeriya sun ce wasu 'yan kunar-bakin-wake sun kai hari a tashar baga da ke birnin.
Rahotanni sun ce an kai harin ne da misalin karfe uku na ranar Litinin.
Ganau sun ce sun ga gawarwakin a kalla mutane 23 wadanda suka mutu sakamakon harin.
Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai a baya kungiuar Boko Haram ce ke daukar alhakin kai irin wadannan hare-haren.