RUKAANAH : Wani Qaton sadauki ne daga cikin Banu Quraish. Gwarzo ne wajen Kokuwa, tunda yake ba'a ta'ba kayar dashi ba..
Rannan sai yace ba zai Musulunta ba, har sai in Manzon Allah (saww) ya yarda yayi kokuwa dashi. Idan ya kayar dashi to zai musulunta.
Nan take Manzon Allah (saww) ya Wujijjigashi, ya kayar dashi Qas hat sau uku.. amma da yake bashi da rabon Imani, sai girman kai ya hanashi Musulunta...
UBAYYU BN KHALAF : Wani Qaton kafiri ne daga cikin Mushrikan Makkah. Kullum idan hanya ta biyo dashi kusa da Manzon Allah (saww) sai yace : "Sai na kasheka Ya kai Muhammadu!!".
Sai Ma'aiki (saww) yace masa : "BARI DAI NINE ZAN KASHEKA IN ALLAH YA YARDA".
Sai aranar yakin Uhudu, bayan an kammala yakin, sai ya fito yace zai tari Manzon Allah (saww).
Har Sahabbai sun shirya zaau tareshi Sai Manzon Allah (saww) yace "A'A KU KYALENI IN TARESHI. AKWAI ALKAWARIN DA MUKAYI NI DASHI".
Ya karbi wani MASHI ya rike ahannunsa. Da ya wurga ma wannan kafirin, Mashin ya Chaki gefen Tumbinsa... Wajen ma bai yi jini ba..
Amma Kafirin nan ya rika Gunji yana kururuwa.. Sai sauran Kafiran suka ce masa "KAITONAK YA UBAYYU!! YANZU WANNAN 'DAN KANKANIN RAUNIN KAKE YI MA EEHU HAKA??".
Sai yace "WALLAHI BALA'IN CIWON DA NAKE JI AWANNAN RAUNIN DA KUKE GANI, DA ACE ZA'A RABA MA DUKKAN MUTANEN QASAR MAKKAH DIN NAN SAI YA ISHESU BAKI DAYA!!".
Akan hanya wannan kafirin ya mutu kafin a karasa dashi Makkah..
YA ALLAH YI SALATI GA MAI KARFI DA KARFIN QUDURA, SAYYIDUNA MUHAMMADUR RASULULLAHI (SAWW) TARE DA IYALAN GIDANSA TSARKAKA. Albarkacin wannan salatin ka Qara mana karfin Imani da tasleemi gareshi, ka kiyayemu daga dukkan sharrin ma'abota Sharri.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.