Wallahi yawancin Mutanen da suke aikata mugayen laifuka, Matayensu sun sani.
Matansu sun san cewa:
Mijinsu ba ya sallah,
Ko Mijinsu Mazinaci ne,
Ko Mjinsu Mashayin giya ne,
Ko Mijinsu 'Dan luwadi ne.
Ko Mijinsu MATSAFI ne.
Amma ba zasu yi musu wa'azi ba, kuma ba zasu fa'da ba, Ba zasu yi musu tawaye ba, Saboda Kwadayin samun abin duniyar da mazajen suka mallaka.
Wani lokacin ma iyayensu da surukansu sun san halin da ake ciki, amma ba zasu yi maganin abun ba, saboda Kwadayin abin da yake basu na kudade da motoci da sauransu.
Duk wanda ya tabbatar da afkuwar wata 'barna, yana da ikon hanawa, amma yayi shuru bai yi magana ba, to laifinsa daidai yake da na masu aikata laifin.
Kuma zaku mutu ku tarar da Allah.