Likitoci da jami'an kasar Indiya sun ce basu taba ganin irin wannan yanayin tsanannin zafin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane har 1,500 ba.
Andhra Pradesh, wani likita ne a jihar da lamarin ya fi tsananta a kudancin kasar ya ce, ba a taba ganin irin yawan mutanen da kafin a kawo su asibiti sun riga sun mutu ba.
Wani babban jami'i na kasar ya ce ana fatar shigowar damuna cikin 'yan kwanaki zai kawo saukin al'amarin.
Mutane da dama sun sayar da rayuwarsu suna shiga rana, saboda suna da bukatar aiki domin su ci abinci duk da tsananin zafin da ake fama da shi.
Title :
Zafi ya hallaka mutane 1,500 a Indiya
Description : Likitoci da jami'an kasar Indiya sun ce basu taba ganin irin wannan yanayin tsanannin zafin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane har 1,500...
Rating :
5