Kamfanin sadarwa na salula mafi girma a Najeriya, MTN, ya yi gargadin cewa maiyiyuwa ya rufe wasu tashoshin sadarwarsa saboda karancin man fetur da iskar gas a kasar.
A wata sanarwar da ya bayar a shafinsa na Twitter, kamfanin ya ce injunansa na dogara ne akan janaretoci saboda rashin wutar lantarki.
Ya ce karancin man fetur kuma ya sanya wasu janaretocin za su daina aiki a cikin awowi kadan masu zuwa.
Kimanin 'yan Najeriya miliyan 55 ke amfanin da tashoshin MTN a wayar salularsu.
Najeriyar dai na fama da tsananin karancin man fetur saboda takaddamar da ake samu tsakanin gwamnati da masu jigilar mai zuwa kasar da kuma yajin aikin da wasu ma'aikatan mai ke yi.
Karancin man na durkussan da harkoki kasuwanci da na rayuwar jama'a a sassa daban daban na kasar.
Hakan dai ya zo ne kwanaki kadan kafin shugaba mai-barin-gado Goodluck Jonathan ya mika mulki ga shugaba mai-jiran-gado Muhammadu Buhari a ranar Juma'a mai zuwa.